Zuwa da mata zauren majalisa: Mahaifina ya mutu ya bar 'ya'ya fiye da 40 - Hon. Alasan Doguwa

Zuwa da mata zauren majalisa: Mahaifina ya mutu ya bar 'ya'ya fiye da 40 - Hon. Alasan Doguwa

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado-Doguwa, ya kushe masu kalubalantarsa a kan nuna matansa da yayi a majalisar tare da sanar da cewa yana da 'ya'ya 27.

Ado-Doguwa, ya ce yana daga cikin sunnar Annabi auren mata da yawa kuma wannan abu ne da 'yan Arewa suka saba yi ballantana Musulmai Hausa da Fulani.

Kamar yadda ya ce, mahaifinsa ya rasu ne 2019 yana da shekaru 86 kuma ya bar 'ya'ya sama da 40. A halin yanzu akwai mai shekaru hudu.

Ado-Doguwa, dan majalisa ne da ke wakiltar mazabar Tudun-Wada/Doguwa ta jihar Kano kuma ya kasance a majalisar ne tun daga 1999, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

A ranar 29 ga watan Janairu na 2020 ne aka rantsar da Doguwa bayan an sake zabe a mazabarsa.

Mutane sunyi ta cece-kuce bayan da Doguwa ya gabatar da matansa hudu da yara 27 a zauren majalisa yayin mika godiya ga jam'iyyar APC da kuma mambobin majalisar, lamarin da ya jawo ihu da sowa tare da tafi daga 'yan majalisar.

Kakakin majalisar, wanda ya datse shugaban masu rinjayen ta hanyar tambayarsa yara 27 ya ce kuma yana fatan samun wasu? Wannan tsokacin ya jawo dariya daga 'yan majalisar.

Mahaifina ya rasu yana da shekaru 86 da 'ya'ya sama da 40 - Ado Doguwa
Mahaifina ya rasu yana da shekaru 86 da 'ya'ya sama da 40 - Ado Doguwa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ina busar iska zan saki bidiyon kaina tsirara - Nafisa Abdullahi

Daga bisani Ado-Doguwa ya nemi gafarar Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ta yadda ya mallaki mata hudu inda shi kuwa yake da daya tak.

Dan majalisar ya ce ya matukar shan mamaki da irin martanin da jama'a ke masa a kan mallakar mata hudu tare da yara 27. A cewarsa, idan dan kudancin kasar nan ya yi masa kallon mamaki, toh ba zai ji komai ba. Amma abin mamakin shine yadda wasu 'yan Arewa kuma Hausa Fulani suka dau lamarin bayan sun tashi a gidajensu sun ga ana yi.

A cewarsa, "Mahaifina ya rasu yana da shekaru 86 kuma ya bar yara sama da 40. A cikinsu kuwa akwai mai shekaru hudu wanda nake kula dasu kuma zan ci gaba. Ina takamar auran mata hudu tare da tara yara 27. Ina kuma fatan samun wasu nan gaba. A matsayina na Musulmi na san ba dabara ta bace ke ciyar dasu ba. Ubangiji ne ke ciyar dasu ta hanyata. Ba zan dau tozarci daga jama'a ba a kan hakan. Mata na da yarana halastattu ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel