Saurayi ya ci 100m a cacar da ya shiga da kudin budurwarsa 10k, rigima ta barke bayan ya bata iya kudinta 10k

Saurayi ya ci 100m a cacar da ya shiga da kudin budurwarsa 10k, rigima ta barke bayan ya bata iya kudinta 10k

Wani mutum da ke Kawempe a kasar Uganda ya shiga bakin duniya bayan da dadaddiyar soyayyar shi da budurwar shi ke niyyar tsinkewa saboda naira miliyan 40.

Wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar tuwita mai suna @Yemihazan ne ya wallafa. Mutumin ya saci naira dubu goma bayan ya ziyarceta. Ta manta da kudin ne a kan gado kafin ta tafi wajen wanke kai.

Saurayin ya kwashe kudin inda ya zuba su a caca wacce cikin kwana biyu ya ce zai biyata. Bayan sa’ar da ya samu, ya samu makuden kudi har naira miliyan 100.

Bayan tsananin jin dadi da farin ciki, ya sanar da budurwarshi amma sai rigima ta balle. Budurwar ta bukaci naira miliyan 40 daga cikin kudin da ya samu.

DUBA WANNAN: Abinda yasa rigingimu suka dabaibaye yankin arewa - Dogara

Saurayin ya ce ba zai bada kudin har haka ba don yayi alkawarin biyanta dubu gomanta ne da ya ara. Zai yi amfani da kudin ne don bunkasa kasuwancinsa amma zai iya ba ta naira miliyan biyar.

Daga nan ne fa budurwar ta yanke shawarar rabuwa da shi kwata-kwata saboda ta ce ya cuceta in har ta karba wannan kudin.

Saurayin ya shiga mawuyacin hali saboda bai shirya ba ta naira miliyan arba’in ba kuma yana kaunar budurwarshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel