Tashin hankali: Ladani ya bawa makwabcinsa zakami ya sha ya mutu

Tashin hankali: Ladani ya bawa makwabcinsa zakami ya sha ya mutu

- Jami’an ‘yan sanda a garin Zuba da ke birnin tarayya a Abuja sun damke wani ladani mai suna Muhammad Lawan

- Ana zargin ladanin ne da hannu wajen mutuwar makwabcinsa mai suna Ibrahim Rabo bayan ya bashi itacen zakami

- Ladanin ya musanta zargin da ake mishi don ya ce ajiye itacen yayi a kan Katanga shi kuwa makwabcin nashi ya dauka ya ci har ya mutu

Jami’an ‘yan sanda a garin zuba da ke birnin tarayya a Abuja sun kama wani Ladani mai suna Muhammad Lawan. An zarge shi ne da sa hannu a rasuwar makwabcin shi ta hanyar ba shi ‘ya’yan itacen zakami wanda ya ci a matsayin magani.

Wanda ake zargin da mamacin mai suna Ibrahim Rabo makwabtan juna ne a kasuwar kayan marmari ta Abuja da ke garin Zuba. Suna kasuwanci tare ne da kuma kula da wani masallaci.

Tashin hankali: Ladani ya bawa makwabcinsa zakami ya sha ya mutu
Tashin hankali: Ladani ya bawa makwabcinsa zakami ya sha ya mutu
Asali: Facebook

A ranar Talata ne aka yi jana’izar wanda ya rasun bayan ya kwanta jinyar kwanaki biyu.

Wani wakilin aminiya Daily Trust da ya samu zantawa da shi a kasuwa, ya ce wanda ake zargin na kula tare da ba wani itacen zakami ruwa ne a gefen kasuwar.

Wakilin aminiya ya samu wanda ake zargin a ofishin ‘yan sanda bayan an kama shi. Ya musanta zargin da ake mishi na ba makwabcin shi maganin da hannun shi. Ya ce ya ciro kwallon zakamin ne a kusa da kwarin inda ya je fitsari.

KU KARANTA: Budurwa ta firgita mutumin da zai yi mata fyade, bayan ta gaya masa cewa tana da cutar Corona

“Na ajiye shi a kan Katanga sai aka samu akasi shi kuma ya dauka ya balla kadan daga jikin kwallon,” in ji shi.

An gano cewa marigayin da farko ya cire kayan jikin shi ne tare da shiga dimuwa tun a ranar farko. Daga bisani ne aka killace shi tare da sanya mishi ruwan magani.

Babban jami’in ‘yan sandan Zuba, CSP Muhammad Yahaya ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce zasu mika mutumin hedkwatarsu a Abuja da zarar sun kammala binciken farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel