Buratai ya baje ma yan majalisa bayanai game da dalilin ruruwar matsalar tsaro a Najeriya

Buratai ya baje ma yan majalisa bayanai game da dalilin ruruwar matsalar tsaro a Najeriya

Manyan hafsoshin tsaron kasa sun bayyana ma majalisar wakilai cewa akwai hannun kasashen waje a cigaba da ruruwar matsalolin tsaro a Najeriya, musamman matsalar ta’addanci da sauran kalubalen tsaro.

Daily Trust ta ruwaito manyan hafsoshin tsaron sun bayyana haka ne yayin wata ganawar sirri da suka yi da kwamitin tsaro ta majalisar wakilai, kamar yadda shugaban kwamitin, Babajimi Benson ya bayyana ma manema labaru.

KU KARANTA: Sana’a sa’a: Gwamnati na neman matasa masu sana’ar hannu domin fara aiki a kasar Jamus

Buratai ya baje ma yan majalisa bayanai game da dalilin ruruwar matsalar tsaro a Najeriya
Manyan hafsoshin tsaro
Asali: UGC

Babajimi yace hafsoshin tsaron sun yi bayanai da dama game da tsaro, don haka akwai bukatar zama a tattaunasu daya bayan daya, muhimmi daga ciki shi ne akwai yiwuwar sa hannu daga kasashen waje a rikicin.

“Akwai ISIS, akwai ISWAP, wadannan wasu abubuwa ne dake bukatar mu tattaunasu a asirce, amma abin da muke so yan Najeriya su sani shi ne mun dukufa dari bisa dari don ganin mun taimaki Sojoji da hukumomin tsaro wajen shawo kan matsalar tsaro cikin kankanin lokaci.” Inji shi.

Haka zalika a cikin wata tattaunawa da babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi da majiyar Legit.ng, ya bayyana cewa manyan hafsoshin tsaron tare da majalisar dokoki sun amince da yin aiki tare don kawo karshen matsalar tsaro.

“Kuna sane da koke koken da ake samu game da matsalar tsaro a duk fadin kasar nan, musamman farfadowar Boko Haram a yankin Arewa maso gabas, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso yamma da sauran miyagun ayyuka, duka wadannan abubuwa ne masu tayar da hankali.

“Mu kanmu mun damu kamar yadda kowanne dan Najeriya yake cikin damuwa, haka zalika gwamnati, a kokarinta na zartar da ikonta, majalisa ta ga akwai bukatar tattaunawa tsakaninmu, wannan shi ne dalilin gayyatarmu.

“A gaskiya mun tattauna matsalolin, sun bamu dama mun bayyana musu tushen matsalar da kuma hanyoyin warware matsalar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng