Yan matan Chibok su 100 sun yi bore a jami’ar Atiku Abubakar dake jahar Adamawa
Akalla yan matan Chibok su 100 da Boko Haram ta taba sacesu, daga bisani ta sako dake karatu a jami’ar Amurka ta Najeriya dake Yola, mallakin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, sun yi bore da zanga zanga a kan tsauraran dokokin abinci a makaranta.
Daily Trust ta ruwaito daliban sun bayyana damuwarsu ne bayan jami’an makarantar sun kwace kayayyakin abinci daga hannunsu, wadanda suka ce an haramta amfani dasu a dakunan dalibai, kamar su lemun kwalba da kayan kwalam.
KU KARANTA: Da dumi dumi: Annobar zazzabin Lassa ta kashe mutane 2 a jahar Katsina

Asali: Depositphotos
Wannan ne yasa daliban suka fara bore a daren Talata har zuwa wayewar garin Laraba, 5 ga watan Feburairu, inda suka tattara kayayyakinsu da nufin zasu fice daga makarantar gaba daya saboda a cewarsu an takura musu.
An samu yamutsi sosai a kofar shiga jami’ar yayin da jami’an tsaro suka hanasu fita daga harabar makarantar, da kyar da sudin goshi aka lallashesu suka koma dakunansu bayan wata ganawar gaggawa da suka yi da shuwagabannin makarantar.
Bayan amsosu daga hannun mayakan Boko Haram ne sai gwamnatin tarayya ta dauki nauyin yan matan domin su yi karatun sharan fagge a jami’an AUN da nufin duk wanda ya samu kyakkyawar sakamako zai haura karatun digiri a jami’ar.
Wata sanarwa daga bakin mataimakin shugaban jami’ar, Abba Tahir ta bayyana cewa an shawo kan rikicin biyo bayan zama da aka yi tsakanin yan matan na Chibok da kuma hukumar makarantar.
Sanarwar ta ce: “Za mu gana da daliban sharan fagge da suka fito daga Chibok domin lalubo hanyoyin ingantan walwalarsu tare da sanar dasu yadda jami’ar AUN take, kamar yadda muka yi ma masu daukan nauyinsu, ma’aikatar kula da harkokin mata alkawari.“
Daga karshe sanarwar ta karkare da cewa manufofin tsarin sharan faggen shi ne warkar dasu daga damuwar da suka shiga a baya, ingantan iliminsu da kuma sake mayar dasu cikin al’umma ba tare da fuskantar tsangawama ba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng