Taskar Kannywood: Sani Danja ya yi korafi game da rufe kamfaninsa da gwamnatin Kano ta yi

Taskar Kannywood: Sani Danja ya yi korafi game da rufe kamfaninsa da gwamnatin Kano ta yi

Shahararren tauraro a masana’antar shirya fina finan Hausa ta Kannywood, Sani Musa Danja ya zargi gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da rufe wani sabon kamfaninsa saboda bambancin siyasa dake tsakaninsu.

BBC Hausa ta ruwaito Danja ya zargi gwamnatin Ganduje ta hannun hukumar tace fina fina a jahar Kano ta rufe masa kamfanin da ya bude na daukan hotuna saboda siyasa, sai dai hukumar ta musanta wannan zargi, inda tace jarumin bai yi ma kamfaninsa rajista ba.

KU KARANTA: Mutane 6 sun mutu a sanadiyyar harin yan bindiga a jahar Kaduna

Tun ba yau ba, Sani Danja ya yi suna wajen goyon bayan jam’iyyar PDP da kuma tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, don haka baya tare da jam’iyyar APC da Gwamna Ganduje.

Danja ya ce, "Babu wata maganar yin rijista, akwai da ma mutanen da ake hakonsu saboda dalilai na siyasa. Kuma ni ina gaya wa mutane cewa su rika ganewa bambancin siyasa alheri ne; idan kana abu wanda babu wanda zai kalubalance ka abubuwa ba za su tafi daidai ba."

Sani Danja ya tabbatar da cewa ya yi rijista da dukkan hukumomin da ke kula da harkokin kasuwanci kafin kamfanin daukar hoton ya fara aiki, daga ciki har da hukumar rijstar harkokin kasuwanci ta Najeriya, Corporate Affairs Commissioin.

Sai dai shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Malam Isma'ila Na'abba Afakallah ya bayyana cewa babu wata makarkashiyar siyasa game da rufe kamfanin Sani Dan, yana mai cewa rashin yin rijista ne.

"Babu wani gida [na daukar hoto] da muka rufe don yana daukar hoto; mai yiwuwa idan gidan daukar hoton wanda kake magana a kai [Sani Danja] ya fado cikin wadanda basu yi rijista ba, to an rufe shi." Inji shi.

Afakallah ya kara da cewa ba kamfanin daukar hoton Sani Danja kawai hukumar ta rufe ba, yana mai cewa sun rufe daruruwan gidajen daukar hoto da basu yi rijista ba, ba tare da la'akari da jam'iyyar siyasar da suke yi ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel