Hukumar ICPC ta fitar da bayani game da daukan mutane 220 aiki cikin dubu 376 da suka nema

Hukumar ICPC ta fitar da bayani game da daukan mutane 220 aiki cikin dubu 376 da suka nema

Hukumar yaki da rashawa da dangoginsu, ICPC, ta fitar da wani sanarwar dake dauke da sabbin bayanai game da aikin da ta sanar da za ta dauka a cikin sabuwar shekarar 2020, wanda a kwanakin baya ta sanar ma yan Najeriya masu sha’awa su nema.

Hukumar ta bayyana cewa biyo bayan kulle amsan takardun masu sha’awar aikin, ta kidaya mutane 376,631 daidai da suka nuna sha’awarsu na yin aiki a cikinta, sai dai hukumar ta kara da cewa gurabe 220 take dasu kacal.

KU KARANTA: Matashin da ya tafi Kano daga Katsina a kasa saboda Ganduje ya samu kyakkyawar tarba

Legit.ng ta ruwaito ICPC ta bayyana haka ne a shafin ta na dandalin sadarwar zamani na Facebook, inda tace akwai ire iren mutanen da take bukatar dauka daga cikin wadanda suka nemi ayyukan, daga cikinsu akwai wadanda suka karanci kididdigar kudi, sharia, tsimi da tanadi, kimiyyar kwamfuta, lissafi, jarida, zane, da sauran manyan kwasa kwasai.

Bayan kammala tantancewa tare da zakulo wadanda suka karanci wadannan kwasa kwasai, hukumar za ta aika musu da sakonni dake nuna sun tsallake matakin tantancewa na farko, daga nan kuma zasu zana jarabawa ta na’urar kwamfuta, sai kuma jarabawar takarda da alkalami, daga nan sai zuwa matakin tambayar yar kure.

Bugu da kari duk wanda ya tsallake dukkanin matakan tankade da rairayan da hukumar ta sanya, za’a sake duba sahihancin takardunsa da kuma bin diddigin asalinsa, haka zalika za’a tarasu a wani sansani domin samun horo na tsawon watanni 6 don tabbatar da lafiyarsu.

A wani labarin kuma, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa akwai shirin daukan sabbin zaratan Sojoji nan bada jimawa ba a kokarin gwamnatin Najeriya na kara adadin jami’an tsaro domin su kawar da matsalar tsaro a kasar.

Osinbajo ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 3 ga watan Feburairu yayin da ya karbi bakoncin wasu Fastoci a karkashin kungiyar fastocin yankin Arewacin Najeriya masu rajin kawo zaman lafiya a yankin.

Osinbajo ya bayyana cewa: “Muna yin duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen matsalar tsaro, muna tafiyar da tsaron nan yadda ya kamata, daga ciki har da aika Sojoji bakin daga domin yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

“Har ma a yanzu zamu kara daukan sabbin Sojoji a rundunar Sojan kasa, kuma zamu dauke su ne a tsarin gaggawa, kuma zamu sayi karin makamai da sauran kayan aiki. A zaman karshe da muka yi na majalisar tsaro mun tattauna yiwuwar kara yawan Sojoji.

“Mun tattauna yadda zamu hada kai da matasa jarumai yan sa kai da sauran yan banga, don haka muna aiki tukuru wajen tsaurara matakan tsaro, musamman yadda zamu yi amfani da na’ura wajen leken asiri a kasar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel