Matashin da ya tafi Kano daga Katsina a kasa saboda Ganduje ya samu kyakkyawar tarba

Matashin da ya tafi Kano daga Katsina a kasa saboda Ganduje ya samu kyakkyawar tarba

Matashin nan dan asalin jahar Katsina da ya kuduri aniyar gudanar da tattaki tun daga jahar Katsina har zuwa jahar Kano saboda kaunar da yake ma gwamnan jahar Kano, ya cika burinsa, kamar yadda za ku gani.

Matashin mai suna Nura Aliyu Batsari ya isa jahar Kano ne a ranar Litinin, 3 ga watan Feburairu bayan kwashe kwanaki uku yana cin hanya shi kadai a kokarinsa na isa birnin Kano.

KU KARANTA: Karin albashi: Kungiyar kwadago ta umarci ma’aikatan gwamnati su fara yajin aikin dindindin

Matashin da ya tafi Kano daga Katsina a kasa saboda Ganduje ya samu kyakkyawar tarba
Nura da Gawuna
Asali: Facebook

A ranar Juma’a, Nura ya fara tattakin nasa daga kofar shiga garin Katsina, watau ‘Welcome to Katsina’, inda ya bayyana manufar tafiyar ita ce don taya Gwamna Abdullahi Umar Ganduje murnar samun nasara a kotun koli a zaben gwamnan jahar.

A kan hanyarsa, Nura ya yada zango a masarautare Bichi domin taya sabon Sarkin Bichi, Mai martaba Aminu Ado Bayero murnar samun wannan sarauta, tare da taya shi murnar karban sandan girma.

Da shigarsa jahar Kano aka sanar da jami’an gwamnati, inda suka fara shirye shiryen tarbarsa a fadar gwamnati, kuma Isarsa ke da wuya ya zarce fadar gwamnatin kai tsaye, inda ya samu kyakkyawar tarba daga mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna.

Matashin da ya tafi Kano daga Katsina a kasa saboda Ganduje ya samu kyakkyawar tarba
Nura da Gawuna
Asali: Facebook

Gawuna ya tarbi Nura ne sakamakon gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi tafiya, inda ya halarci bikin kaddamar da littafin tarihin rayuwar wani babban Alkalin kotun koli, mai sharia Amiru da ya yi murabus daga aiki bayan cika shekaru 70 a rayuwa.

Nura ya samu rakiyar 'yan majalisun dokokin jahar katsina guda biyu, da kuma wasu daga Jami an gwamnatin Katsina da' yan social media na jihar Katsina a yayin da Gawuna da sauran jami’an gwamnatin jahar Kano suka tarbe shi.

A wani labarin kuma, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Batagarawa/Charanchi/Rimi a majalisar wakilan Najeriya, Alhaji Hamza Dalhatu ya rasa matarsa a wani mummunan hadarin mota da ya auku a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan hadari ya faru ne da yammacin Lahadi, 2 ga watan Feburairu, yayin da matar dan majalisar mai suna Hajiyar Maryam ta rasu a ranar Litinin, 3 ga watan Feburairun shekarar 2020.

Wata majiya ta karkashin kasa ta shaida ma majiyarmu cewa an yi kokarin ceto rayuwar Hajiya Maryam ta hanyar garzayawa da ita zuwa wani Asibiti dake garin Abuja, amma koda aka isa ta fita cikin hayyacinta, daga bisani kuma aka sanar da mutuwar ta ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel