Mai garkuwa da mutane ya zargi abokansa da karya a gaban kotu, ya bukaci su ji tsoron Allah

Mai garkuwa da mutane ya zargi abokansa da karya a gaban kotu, ya bukaci su ji tsoron Allah

Wani abin mamaki ya faru a ranar Litinin cikin babbar kotu da ke Yola. Daya daga cikin mutane 8 da ake zargi da garkuwa da mutane ne ya amsa laifinsa tare da kira ga sauran bakwai din da suka ki amsawa da su ji tsoron Allah su fadi gaskiya.

An gurfanar da wadanda ake zargin ne a kotun karkashin jagorancin mai shari'a Nathan Musa.

Rufai Ahmadu tare da Mohammed Abdullahi sun amsa laifinsu a gaban kotun ne bayan da aka zargesu da garkuwa da mutane. Amma kuma sunyi kira ga sauran wadanda aka gurfanar dasu tare da su dena karya.

"Ku daina karya, dukkanmu akwai sa hannunmu," Ahmadu ya fadi da harshen Hausa.

Sauran wadanda aka gurfanar dasu tare su din sun hada da: Yusuf Abubakar, Yahaya Sani, Umar Jalo, Abdullahi Ibrahim, Ishaku Umar, Muhammed Adamu da Bala Sani.

Hukumar Jami'an tsaro ta fararen kaya ce ta kama su tare da gurfanar dasu a kan laifuka shida da suka hada da garkuwa da mutane tare da satar shanu, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fada wa Lawan da Gbajabiamila a kan tsaro yayin ganawarsu

An zargesu ne da yin garkuwa da wani Alhaji Waziri Ibrahim wanda suka je har gidansa da ke Shagari Quarters a Yola suka yi awon gaba dashi a ranar 26 ga watan Disamba 2019. Sun karba naira miliyan daya da dubu dari shida daga hannun iyalansa na kudin fansa.

Hakazalika an zargesu da garkuwa da wani Dr Kawiyo Abdurrahman da ke Lakare a Yola a ranar 5 ga watan Janairu tare da karbar naira miliyan daya da dubu dari hudu a matsayin kudin fansa.

An gano suna da sa hannu a satar wasu shanu da aka yi a karamar hukumar Mayo Belwa ta jihar Adamawa.

Mai shari'ar ya dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Fabrairu.

Ya bada umarnin a adana wadanda suka amsa laifinsu a hannun jami'an tsaron farin kaya. Sauran da basu amsa ba kuwa a mika su gidan gyaran hali na jihad Yola, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel