Buhari ya kafa kwamitin da zai duba halin rashin tsaro a cikin kasa

Buhari ya kafa kwamitin da zai duba halin rashin tsaro a cikin kasa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti don duba kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta

- 'Yan kwamitin zasu hada ne da 'yan majalisar tarayya da kuma 'yan jam'iyyar APC

- Shugaba Buhari na fuskantar kalubale ne sakamakon habakar rashin tsaro a fadin kasar nan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin da zai dinga duba halin da tsaron kasar nan ke ciki akai-akai.

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana hakan bayan ganawar da suka yi tare da shugaban kasar da kuma shugaban majalisar dattijan kasar nan.

Gbajabiamila ya sanar da manema labaran gidan gwamnati cewa 'yan kwamitin zasu hada ne da zababbu, 'yan majalisa da kuma 'yan jam'iyyar APC.

Ya ce kwamitin zai tallafa wajen shawo kan matsalar tsaron kasar nan baki daya.

A yayin da aka tambaye shi a kan yadda wasu daga cikin 'yan Najeriya suka bukaci a sauke shugabannin tsaron kasar nan, Gbajabiamila ya ce: "Ra'ayoyi sun rabu amma mafi rinjaye shine a saukesu. Wannan shine ya zamo abun tattaunawarmu a majalisar wakilai da dattijai."

Buhari ya kafa kwamitin da zai duba halin rashin tsaro a cikin kasa
Buhari ya kafa kwamitin da zai duba halin rashin tsaro a cikin kasa
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fada wa Lawan da Gbajabiamila a kan tsaro yayin ganawarsu

Ya kara da cewa, "Da yawa daga cikinmu sun ce sai an dau mataki kwakwara. Wasu kuwa sun ce tunda maganar garkuwa da mutane da kashe-kashe ake yi, me ya shafi soji? Tambayar a nan ita ce, idan aka sauya shugabannin tsaro, hakan zai shawo kan garkuwa da mutane da kashe 'yan Najeriya da ake yi?

"Amfanin sojin Najeriya shine tsaron waje ba cikin gida ba. 'Yan sanda ne ke tsaron cikin gida da kuma irin kalubalen da muke fuskanta."

Kakakin majalisar ya ce, kwamitin zai dinga duba tsaron ne lokaci zuwa lokaci. Za ta yuwu sau daya a mako guda ko a makonni biyu.

A bangarensa, Lawan ya ce shugaban kasar ya damu matuka a kan tabarbarewar tsaron kasar nan.

Ya ce: "mun gana da shugaban kasar ne a kan matsalar tsaron kasar nan da sauran al'amuran mulkin kasar nan. Kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta a cikin kwanakin nan yasa dole muyi aiki tare."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel