Maryam Sanda: Kungiya ta kalubalanci hukuncin kotu, ta nuna alamar samun nasara a kotun koli

Maryam Sanda: Kungiya ta kalubalanci hukuncin kotu, ta nuna alamar samun nasara a kotun koli

A cewar wani mai rajin kare hakkin dan Adam mai suna Lemmy Ughegbe, Jastis Halilu ya yi gaggawa ta yadda ya yanke hukunci ba tare da ya saurari sukar farko ba, wanda hakan ke bayyana rashin inganci a kan hukuncin kotun.

Masu tsaron gidan gyaran hali sunyi awon gaba da Maryam Sanda daga babbar kotun tarayya a Abuja bayan an yanke mata hukuncin kisa a ranar 27 ga watan janairu, 2020.

Wani mai rajin kare hakkin dan Adam kuma daraktan sadarwa na Advocacy of make a difference initiative, Lemmy Ughegbe, ya koka da yadda Jastis Halilu ya kasa bin shari'ar a hankali kafin yankewa Maryam Sanda hukunci kan kisan mijinta, Bilyaminu Bello.

A yayin zantawa da Arise News, mai rajin kare hakkin dan Adam din ya ce Jastis Halilu, wanda ya kwatanta da "alkali mai kwarin guiwa" bai yi shari'ar yadda ta dace ba.

Ughegbe ya ce rashin hukunci ta bangaren abinda lauyan wacce ake kara ya sanar ya bayyana cewa alkalin ya bi bangare daya ne, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

Maryam Sanda: Kungiya ta kalubalanci hukuncin kotu, ta nuna alamar samun nasara a kotun koli
Maryam Sanda: Kungiya ta kalubalanci hukuncin kotu, ta nuna alamar samun nasara a kotun koli
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kwantar da tsohon ministan Buhari a asibiti, ya nemi 'yan Najeriya su taya shi da add'ua

Ya ce, "Na shawarce su a kan su daukaka kara don wannan doka ce. Wannan hukuncin kisan dole ya tashi. Babu wanda ake yankewa hukuncin kisa babu kwakwaran shaida kuma ba tare da anji tare da yanke hukunci a kan abinda mai kare shi ya ce ba."

"Rashin samun makamin da aka yi kisa da shi, rahoton dalilin mutuwar shi wanda aka binciki gawarsa, takardar da ta amsa laifinta da kuma hotunan jikin mamacin duk zasu iya hana yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa." ya kara da cewa.

Mai rajin kare hakkin dan Adam din ya ce alkalin bai yi aikin da aka sa shi ba na duba shaidun kowanne bangare amma sai ya bige da yanke hukunci bayan sauraro da amfani da bangare daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel