Yaki da ta’addanci: Rundunar Sojan sama ta tura wani sabon jirgi yaki zuwa Maiduguri

Yaki da ta’addanci: Rundunar Sojan sama ta tura wani sabon jirgi yaki zuwa Maiduguri

Babban hafsan Sojan sama, Air Marshal Sadique Abubakar ya bayyana cewa rundunar Sojan saman Najeriya za ta aika da wani sabon jirgin yaki kirar C130 zuwa yankin Arewa maso gabas domin taimakawa a yaki da ta’addanci.

Daily Trust ta ruwaito wannan sabon shiri na rundunar Sojan sama baya rasa nasaba da sabbin hare haren da mayakan Boko Haram suke kaiwa a kauyukan garin Maiduguri wanda haka yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

KU KARANTA: Da dumi dumi: An kama ‘kanwa uwar gami’ dake da hannu a kisan Janar Idris Alkali

Sadique ya bayyana cewa za su tura sojoji sabbin jini tare da wannan jirgin yaki zuwa yankin Arewa maso gabas domin baiwa Sojojin rundunar kasar Najeriya taimakon da suke bukata daga sama a yakin da suke yi da yan ta’adda.

Shi dai wannan jirgi ya samu gyara na musamman domin aiki a Arewa maso gabas. “Wannan jirgi na da matukar muhimmanci a aikin da muke yi, kuma muna farin cikin gudanar da duk gyare gyaren da yake bukata da kanmu a gida Najeriya.

“Wannan ne jirgin C-130 na biyu da muka gyara shi a Najeriya, a nan jahar Legas, kuma burinmu shi ne gudanar da garambawul a kan jirgi na uku, NAF-918, kuma ina da yakinin hakan ba zai gagara ba duba da horon da Sojojinmu suke samu, da kuma sauran kwararrun da muka gayyato.” Inji shi.

A wani labari kuma, Wasu mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta kai mummunan hari a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu inda suka tare wata mota dake dauke da fasinjoji, suka yi ma guda uku daga cikinsu yankan rago.

Wata majiya daga rundunar tsaro ta tabbatar mata da aukuwar lamarin, inda yace yan ta’addan sun tare hanyar ne da yammacin ranar Talata, 28 ga watan Janairu a daidai garin Auno na karamar hukumar Konduga.

Majiyar ta bayyana cewa motar fasinjojin ta mutu ne a kan hanyar sakamakon wata matsala da ta samu, wanda hakan ya tilasta ma fasinjojin motar fitowa domin gyaran motar, a daidai wannan lokaci ne Boko Haram suka bayyana.

Isarsu inda fasinjojin suke ke da wuya, sai yan ta’addan suka kwantar da guda uku daga cikinsu, suka musu yankan rago da adda, yayin da na hudunsu yake cikin mawuyacin hali a yanzu haka sakamakon raunin daya samu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel