Samun waje: Wani almajiri da baya karbar sadakar da tayi kasa da naira 500

Samun waje: Wani almajiri da baya karbar sadakar da tayi kasa da naira 500

- Wani mutum mazaunin Fatakwal da ke jihar Rivers ya bayyana gamon shi da wani mai bara a titi

- Ya bada labarin yadda ya ba mabaracin naira hamsin amma sai ya mayar mishi tare da cewa baya karbarta

- Mai barar ya sanar da Chidi cewa daga naira dari biyar zuwa sama kadai yake karba

Wani mutum mazaunin Fatakwal a jihar Rivers ya bada labarin yadda mai bara ya mayar mishi da kudin shi wata rana da ya bada sadaka.

Mutumin mai suna Chidi ya wallafa labarin ne a shafin shi na tuwita, wanda ya jawo tsokaci kala-kala daga jama'a. Ya bada labarin yadda ya ba wani mai bara naira hamsin a Fatakwal amma sai ya dawo mishi da sadakar shi.

Samun waje: Wani almajiri da baya karbar sadakar da tayi kasa da naira 500
Samun waje: Wani almajiri da baya karbar sadakar da tayi kasa da naira 500
Asali: Facebook

Bayan ya ba mabaracin naira hamsin, sai ya ji an damko rigar shi tare da kalubalantar dalilin da yasa zai bashi naira hamsin.

Chidi ya bayyana yadda mai barar ya dawo mishi da kudin shi tare da jaddada mishi cewa daga dari biyar zuwa sama yake karba, kamar yadda jaridar Corretng ta ruwaito.

KU KARANTA: Babbar magana: Allah ya nuna mini cewa ba za a rataye Maryam Sanda ba - Babban Fasto

Wannan abu kuwa ya ba Chidi mamaki don bai yi kasa a guiwa ba ya wallafa labarin a tuwita

Ya rubuta: "Wasu mabaratan sun kai inda ba a tsammani. Na bada sadakar naira hamsin amma sai mai baran ya damko rigata tare da bani kudina. Ya ce ba ya karbar irinsu don daga dari biyar zuwa sama yake karba."

Idan ba zamu manta ba, a jiya ne gidan rediyon freedom da ke jihar Kano suka bayyana cewa gwamnatin jihar Kano za ta hana mata barace-barace a kan titunan jihar.

Wannan ya fito daga bakin daraktar ma'aikatar al'amuran mata ta jihar, Hajiya Kubra ne a tattaunawar da ta yi da filin Barka da Hantsi.

A cewar daraktar, mata basu dace da wannan ci bayan ba kuma gwamnatin jihar Kano na iyakar kokarinta wajen tallafawa da tabbatar da walwalar mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel