Wa'iyazubillah: Na kashe mahaifiyata saboda na dinga kwanciya da mahaifina - Budurwa

Wa'iyazubillah: Na kashe mahaifiyata saboda na dinga kwanciya da mahaifina - Budurwa

- Abin mamaki ba ya karewa amma wannan hauka da karshen duniya ne za a ce

- Wata budurwa wacce ta yi karatu a UK ta bayyana yadda ta kashe mahaifiyarta don ta ci gaba da kwanciya da mahaifinta

- Ta ce tun bayan dawowarta Najeriya ne ta fara kwanciya da mahaifinta amma kuma mahaifiyarta na mata cikas a duk lokacin da take bukatar mahaifin nata

Abin mamaki ba ya karewa a duniya. Wannan ba abun mamaki bane don hauka kawai zamu kira shi da karshen zamani. Sharon 'yar asalin Najeriya ce amma ta yi makaranta a UK.

"Ina son mahaifiyata da mahaifina amma na fi yi wa mahaifina magana ta waya lokacin ina UK. Tun daga nan ne na fara jin wani yanayi game da mahaifina."

Ta ce tana kammala jarabawarta ta hanzarta dawowa gida don hidimtawa Najeriya. Amma kuma sai labari ya canza.

Ta ce wata rana mahaifiyarta ta yi tafiya zuwa Dubai sai ta je dakin mahaifinta don gaishe shi da safe. A nan ne ta ga yadda mazakutar mahaifinta ta mike kuma ta kasa jurewa har sai da ta ja hankalin shi ya yi lalata da ita.

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sanya matan Hausawa ke tsufa da zarar sunyi aure

Daga nan ne kuwa ta ci gaba da kwanciya da mahaifinta.

A wata rana ne sha'awarta ta tashi kuma tana bukatar kwanciya da mahaifinta amma kuma mahaifiyar ta na nan. Ta nuna wa mahaifinta manufarta amma sai ya dinga nuna mata ta kwantar da hankalinta don mahaifiyar ta na nan.

Daga nan ne ta hada musu abin karyawa kuma ta saka wa mahaifiyarta guba a cikin abin shan ta. A haka ta kashe mahaifiyarta don ta ci gaba da more rayuwa tare da mahaifinta, kamar yadda Ireporter online suka ruwaito.

Amma sai mahaifinta ya fusata bayan ya gane ita ta kashe mahaifiyarta kuma ya kira 'yan sanda suka kama ta.

"Ina yin amfani da wannan damar don rokon mahaifina a kan ya yafe min." cewar budurwar.

Wa'iyazubillah: Na kashe mahaifiyata saboda na dinga kwanciya da mahaifina - Budurwa
Wa'iyazubillah: Na kashe mahaifiyata saboda na dinga kwanciya da mahaifina - Budurwa
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel