Girma ya fadi: Uwa ta kwace saurayin diyarta, sun haihu tare

Girma ya fadi: Uwa ta kwace saurayin diyarta, sun haihu tare

Wata mata baturiya ta bayyana cewa ba za ta taba yafewa mahaifiyarta ba sakamakon kunar zuciyar da ta saka ta a ciki. Mahaifiyar ta aure mijin diyarta tare da haihuwa tare da shi.

Matar mai shekaru 34 mai suna Lauren Wall ‘yar asalin Twickenham ce, gari da ke Kudu maso yammacin birnin London. Ta auri mijinta ne tun tana da shekaru 19 a duniya wanda daga baya ya ci amanarta ta hanyar auren mahaifiyarta.

Lauren ta bayyana cewa mahaifiyarta ta kashe zunzurutun kudinta wajen tabbatar da cewa sun yi shagalin aure na kece raini kuma ta bi ma’auratan zuwa yawon bude idon da suka je bayan auren.

Amma kuma shakuwar da ke tsakanin mahaifiyarta da mijinta abin mamaki ne. Duk da bata taba zargin akwai wani abu da ke tsakaninsu ba, amma babu dadewa da aurensu ya bar ta inda ya koma wajen mahaifiyarta.

DUBA WANNAN: Maryam Sanda: Wata matar aure ta sake kashe mijinta a Katsina

A yayin tattaunawa da aka yi da Lauren, ta ce “Paul da mamana suna matukar jituwa amma ban damu ba saboda sirikarsa ce. Bamu dade da aure ba ya barni.”

Lauren ta bayyana yadda kanwar mijinta ta ga wasu sakonni tsakanin mahaifiyarta da tsohon mijinta amma lokacin da ta tinkareta da zancen, sai ta ce mata bata da hankali.

A lokacin da na tinkari Paul da zancen sai muka fara tashin hankali kuma ya hana ni ganin wayarsa,” Lauren ta ce.

Daga nan ne Paul ya cire zoben aurensu kuma ya bar ta da ‘yarsu mai wata bakwai inda ya tare da mahaifiyarta.

A halin yanzu dai har mahaifiyarta ta haihu tare da Paul, lamarin da yasa ta ce ba zata taba yafe mata ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel