Tsohon hadimin shugaba Buhari yace Najeriya ta yi hannun riga da adalci

Tsohon hadimin shugaba Buhari yace Najeriya ta yi hannun riga da adalci

Tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mista Okoi Obono-Obla ya bayyana rashin gamsuwar sa da harkar sharia a Najeriya, inda yace babu wata adalci da mutum zai iya samu a Najeriyar ta yau.

Premium Times ta ruwaito Obla ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Calitown.com inda yace babu adalci a Najeriya ko kadan, musamman duba da yadda ake neman wulakanta shi a matsayinsa wanda ya sadaukar da ransa ga Najeriya.

KU KARANTA: Har yanzu bamu samu kudin fara aikin jirgin kasa na Ibadan zuwa Kaduna ba – Amaechi

Obla wanda Buhari ya nada shi shugaban kwamitin kwato kadarorin gwamnati daga hannun barayin jami’an gwamnati ya fara fuskantar matsala ne a lokacin da hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta fara farautarsa, har ma ta sanar da nemansa ruwa a jallo, amma ya tsere.

“Na sadaukar da rayuwata wajen yaki da zalunci tare da tabbatar da ganin an yi gaskiya da adalci a Najeriya, amma duba da abin da nake gani a yanzu babu adalci a kasar nan. Akwai wasu miyagu masu karfi a zagaye da Buhari.

“A gaskiya koda wani mukami aka bani a yanzu a kan yaki da rashawa a Najeriya, gaskiya ba lallai na amsa ba, koda kuwa za’a bani tsaro saboda a baya na dage kai da fata don ganin na yi abin da ya kamata kamar yadda aikina ya bukata, amma akwai mutanen da bzasu taba bari kasa ta samu alheri ba.” Inji shi.

Obla yace babbar matsalarsa ICPC shi ne tun lokacin da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyanashi a matsayin mutumin dake da cancantar shugabantar hukumar, tun daga nan shugaban ICPC ya sa masa ido.

Sai dai koda aka tuntubi hukumar ICPC kan wannan batu, sai kaakakin hukumar, Rashidat Okoduwa ta musanta zargin, inda tace asali ma ICPC ta bashi daman ya gabatar da kansa gareta domin ya kare kansa daga zarge zargen da ake masa, amma ya tsere.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel