Kotun duniya ta bada umarnin kare rayukan Musulman Rohingya a kasar Myanmar

Kotun duniya ta bada umarnin kare rayukan Musulman Rohingya a kasar Myanmar

Kotun duniya, watau International Court of Justice ta umarci gwamnatin kasar Myanmar da ta dauki matakan kare al’ummar Musulman kasar da ake kira Rohingya daga cin zarafin da ake musu tare da barazana ga rayuwarsu.

Haka zalika kotun ta umarci gwamnatin Myanmar ta tabbatar da kare rayuwar Musulman Rohingya tare da dukiyoyinsu, sa’annan ta tabbata ta adana duk wasu shaidu dake nuni da cin zarafi, wulalanci da kuma kisan gillar da aka yi ma Musulmai a baya.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Yan bindiga sun sace shanu 105 a jahar Filato

Kotun duniya ta bada umarnin kare rayukan Musulman Rohingya a kasar Myanmar
Kotun duniya ta bada umarnin kare rayukan Musulman Rohingya a kasar Myanmar
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito Musulman kasar Gambia ne suka shigar da gwamnatin kasar Myanmar kara gaban kotun a watan Nuwambar da ta gabata biyo bayan kashe kashen da aka yi ma Musulmai a kasar, inda suke zargin Myanmar da aikata laifin kisan kare dangi tare da keta dokar majalisar dinkin duniya na 1948.

Sai dai hukuncin d kotun ta yanke na ranar Alhamis, 23 ga watan Janairu ya takaita ne kawai ga dakatar da gwamnatin Myanmar daga cigaba da kuntata ma Musulmai ta ko ta wani fuska, yayinda cikakken hukunci a kan shari’ar ka iya daukan shekaru da dama.

Alkalan kotun su 17 sun tabbatar ma duniya cewa Musulman Rohingya na cikin hatsari, kuma dole ne a dauki matakin karesu. Jagoran Alkalan a yayin zaman, Abdulbaqwi Yusuf yace:

“Musulman Rohingya na cikin hadarin fuskantar kisan kare dangi. Dole ne Myanmar ta dauki matakan dakatar da wannan mummunan lamari, kamar yadda dokar hana kisan kare dangi na shekarara 1948 ta tanadar.” Inji shi.

Daga karshe mai sharia Abdulbaqwi ya bayyana cewa dole ne gwamnatin kasar Myanmar ta kai ma kotun duniya rahoto game da matakin da ta dauka a kan yan Rohingya cikin watanni hudu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel