Gwamnonin Najeriya sun yi taron gaggawa gabanin babban taron majalsar tattalin arziki

Gwamnonin Najeriya sun yi taron gaggawa gabanin babban taron majalsar tattalin arziki

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta gudanar da wani taro na musamman a daren Laraba, 22 ga watan Janairu gabanin babban taron majalisar tattalin arzikin kasa da zai gudana a ranar Alhamis, 23 ga watan Janairu.

Daily Trust ta ruwaito duk da cewa kungiyar bata bayyana batutuwan da gwamnonin suka tattauna ba, amma majiyoyi sun tabbatar da cewa batutuwan basu wuce game da batun kudaden da gwamnatin tarayya ke cirewa daga kudaden su na wata wata ba.

KU KARANTA: Ba duka aka lalace ba: An karrama Dansandan da bai taba amsan cin hanci ba

Sai dai gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana cire wadannan kudade daga kudin wata wata na jahohin ne domin biyan bashin kudin tallafin da ta basu a baya domin su samu daman cike gibin kasafin kudin jahohinsu.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron gaggawar akwai na Ekiti, Osun, Ondo, Kogi, Kebbi, Filato, Yobe, Neja, Delta, Kaduna, Jigawa da Nassarawa yayin da gwamnonin jahohin Gombe, Borno, Oyo, Anambra, da Enugu suka tura mataimakansu.

A wani labarin kuma, yan Najeriya sun yi diran angulu a kan tsohon Sanatan mazabar jahar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye sakamakon yadda yake ma jama’a gadara tare da kwalelen arzikin daya mallaka, arzikin da suka ce nasu ne ya kwasa.

Dino Melaye ya wallafa wasu hotuna a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda aka hange shi zaune a kan wata kujerar alfarma cikin wani katafaren gida, ya yi ma hotunan taken; “Kada ku tambaye ni ta yaya, ku tambayi Allah wanda Ya yi mani nasibi. Allah mai girma, girma naka ne, Dino Melaye na godiya a kullum.”

Yawancin yan Najeriya da suka yi tsokaci game da wannan hoto sun yi korafi ne, inda suka nuna bacin ransu da yadda yake nuna gadara da isa, sa’annan suka yi kira ga hukumomin yaki da rashawa da su bincike shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel