Budurwa ta kashe makwabcinta ta hanyar caka masa kwalba kan ya rike mata kugu

Budurwa ta kashe makwabcinta ta hanyar caka masa kwalba kan ya rike mata kugu

- A ranar Juma'a ne alkalin wata kotun majistare dake Legas ya bukaci a adana mishi wata mata mai shekaru 35 a gidan gyaran hali

- Ana zargin Stella da laifin kisan makwabcinta mai suna Monday Bella ta hanyar soka mishi kwalba a wuya

- Fada ya sarke tsakaninsu ne bayan da mamacin ya tabawa Stella kugu bayan bata so ba

A ranar Juma'a ne wani alkalin kotun majistare dake Legas ya bukaci a adana mishi Stella Olowofoyekun mai shekaru 35 a gidan gyaran hali. An zargi Stella ne da sukar makwabcinta da fasasshiyar kwalba wacce tayi ajalin shi.

Wacce ake zargin na fuskantar zargin kisan kai ne kuma kotun taki sauraron rokonta.

Alkali Oluwatoyin Oghere ya bukaci a adana wacce ake zargin a gidan gyaran hali dake Legas kafin ya shawarta shari'ar da daraktan gurfanarwa na jihar Legas. A don haka ne aka dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Maris.

Tun farko dai 'yar sanda mai gabatar da kara mai suna Modupe Olaluwoye ta sanar da kotun cewa an aikata laifin ne wajen karfe 11:30 na dare a yankin Mati dake tsibirin maciji a Apapa jihar Legas.

Tace wacce ake zargin ta soki makwabcinta mai suna Monday Bella da kwalba wanda hakan ya kai shi ga mutuwa saboda ya taba ta da wasa.

KU KARANTA: Allahu Akbar: Mutumin da yafi kowa gajarta a duniya ya rasu

Kamar yadda Olaluwoye ta sanar, mamacin ya taba kugun wacce ake zargin ne amma ta bukaci ya dena hakan.

Ta sanar da kotun cewa fada ya sarke wanda yasa wacce ake zargin ta dau fasassar kwalba ta soke shi a wuya da ita.

Tace sauran makwabtan sun hanzarta kai shi asibiti amma ana isa aka tabbatar da mutuwar shi.

Wannan laifin yaci karo da sashi na 222 kuma abun hukuntawa ne a sashi na 223 na dokokin laifukan jihar Legas na 2015.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa sashi na 223 ya tanadi hukuncin kisa ne a kan wannan laifin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel