Manyan limaman coci hudu a Najeriya da asalinsu Musulmai ne

Manyan limaman coci hudu a Najeriya da asalinsu Musulmai ne

Wasu fastoci a Najeriya sun fuskanci abubuwa masu tarin aywa kafin su kai inda suka a halin yanzu. Wasu daga ciki kuwa har sauya addininsu suka yi don bautar Ubangiji. Akwai sanannun fastoci a Najeriya wadanda a farkon rayuwarsuu musulmai ne. Daga cikinsu kuwa a halin yanzu sunyi matukar suna a harkar kira zuwa ga addinin Kirista. Ga kadan daga cikinsu:

1. Fasto David O. Oyedepo: Fasto ne haifaffen da Najeriya kuma marubuci ne. Shi ya kirkiro kuma yake kula da babban cocin Living Faith wacce aka sani da Winners Chapel. An haifesa ne a ranar 27 ga watan Satumba 1954. Ya tashi ne a cikin dangi masu mabanbantan addinai. Sunan mahaifinsa Ibrahim kuma musulmi ne nagari. Mahaifiyarsa sunanta Dorcas kuma mamba ce aa cocin Cherubim and Seraphim Movement.

2. Apostle Johnson Suleiman: Shine mai kual da Omega Fire Ministries International wacce ke da hedwata a Auchi, jihar Edo. Kamar yadda wani labari ya bayyana, wata kungiyar malami ta taba samun iyayensa cewa akwai babban fasto a iyalansu amma basu dau zancen da gaske ba tunda duk musulmai ne. Sun bukaci fastocin da su tafi amma a yau sai gashi wannan hasashen ya cika.

3. Mathew Oshimolowo: An haifesa a ranar 17 ga watan Maris, 1952. Ashimolowo ya bar musulunci inda ya koma addinin Kirista yana da shekaru 20 bayan mutuwar mahaifinsa. Shine babban fasto Kingsway International Christian Center(KICC).

4.Tunde Bakare: Kamar yadda wikipedia ta bayyana, an haifi Bakare ne a musulmi amma ya koma Kirista a 1974. Shine daya daga cikin fastoci wadanda suka fi suna a Najeriya. Ya fito a matsayin mataimakin shugaba Buhari a takarar Buhari na 2011. An san faston da iya caccakar gwamnati kuma yana daya daga cikin fastocin Latter Rain Assembly.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel