Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Uwa da y’ayanta mata 3 sun mutu a gobara a Yobe

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Uwa da y’ayanta mata 3 sun mutu a gobara a Yobe

Hukumar kashe gobara ta jahar Yobe ta tabbatar da mutuwar da yaranta uku dukkaninsu yan mata a cikin a wata wutar gobara da ta tashi a daren Talata a gidansu dake unguwar Red Bricks dake garin Damaturu na jahar Yobe.

Jami’in hukumar, Usman Habu ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarun Najeriya, inda yace: “Da misalin karfe 11 na dare muka samu rahoton tashin gobara a rukunin gidajen Red Bricks dake kan titin Maiduguri na garin Damuturu.

KU KARANTA: Tirka tirkan zabe: Alkalan kotun Koli sun halasta zaben gwamnonin Neja, Abia da Delta

“Koda muka isa gidan sai muka samu rahoton cewa mai gidan, Malam Adamu Aliyu ya yi kokarin ceto iyalan nasa daga wutar, amma sai dansa dan shekara 5 kadai ya iya cetowa sakamakon wutar ta yi karfi sosai babu yadda ya iya sai dai ya kyalesu, shi ma da kyar ya fito daga gidan.

“Da karfi muka balla kofar gidan, inda muka shiga muka tarar da gawarwakin matarsa da yaranta guda uku mata.” Inji shi.

Sai dai Malam Habu ya danganta mutuwar mamatan ga rashin kofar bayan gida wanda za a iya amfani da shi a lokacin gaggawa, don haka ya yi kira ga masu gidaje su tabbata suna fitar da akalla kofofi biyu a gidansu.

Wata makwabciyar mamatan mai suna Malama Binta Mohammed ta bayyana sunayen yaran da suka mutu kamar haka; Aisha Aliyu, Sa’adatu Aliyu da Safiya.

Shi ma likitan asibitin kwararru na garin Damaturu, Dakta Istifanus ya bayyana cewa an kawo masa yaron dauke da kumburarren kashi, amma a yanzu yana samun kulawa a asibitin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel