Babban sojan kasar Amurka ya karbi Musulunci bayan muhawara da wani soja musulmi

Babban sojan kasar Amurka ya karbi Musulunci bayan muhawara da wani soja musulmi

Wani sojan kassar Amurka mai mukamin Laftanal kanal ya koma addinin Musulunci bayan tafka wata muhawara da wani abokin aikinsa soja musulmi a bainar jama'a.

Sojan mai suna Micheal Barnes an haife shi, kuma ya tashi, a cikin dangi masu akidar addinin Kirista a garin Alexandria a jihar Louisiana ta kasar Amurka. A wata makarantar addinin Kirista Barnes yayi karatu kafin daga bisani ya shiga aikin soja yana da shekaru 23 a duniya.

Barnes ya hadu da wani sojan kasar Amurka musulmi mai kuma son addini yayin da aka kaisu wani aiki a kasar Jamus.

Laftanal kanal Barnes, kasancewarsa babban soja, ya kasance mai yawan kalubalantar abokin aikinsa, sojan Amurka musulmi, a kan cewa addinin Kirista gaba yake da na Islama. lamarin da yasa har suka shirya yin muhawara a bainar jama'a.

DUBA WANNAN: Sayen tsohon layin waya da diyar Buhari, Hanan, ta taba amfani da shi ya jawo wa matashi daurin watanni

Bayan kammala muhawarar, sai Barnes ya yanke shawarar fara nazari a kan addinin Islama. Ya kan ware lokaci domin karanta Qur'ani da Bibul a kowacce rana idan ya dawo daga aiki kafin daga bisani ya koma addinin Musulunci bayan shekaru biyu.

Da yake bayyana dalilansa na komawa addinin Islama, Branes yace Qur'ani ya matukar birgeshi musamman karfin guiwar da littafin mai girma ya ba wa jama'a a kan yin tunani a duk abinda zasu yi.

Babban soja Barnes ya karbi kalmar shahadah tare da canja sunansa zuwa Khalid Shabazz.

Yanzu haka Shabazz soja ne mai matsayin Laftanal kanal a rundunar soji ta kasar Amurka sannan yana da digiri na biyu da na uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng