Ba mu yi karin kudin wutar lantarki ba - FG

Ba mu yi karin kudin wutar lantarki ba - FG

Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) ta yi karin haske a kan labarin dake yawo a gari tare da bayyana cewa bata riga ta yi karin kudin wutar lantarki ba.

Usman Arabi, babban manajan hukumar NERC, shine wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da NERC ta fitar a shafinta na yanar gizo, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya samu a jihar Legas a ranar Lahadi.

Arabi y ace: “An jawo hankalin NERC a kan labaran da kafofin yada labarai suke yadawa na cewa an kara kudin wautar lantarki. Muna so mu sanar wa jama’a cewa, wannan Karin ya biyo bayan bukatar da ta bijiro wa hukumar ne tun a 2015.

“Karin ya biyo bayan karancin kudin shiga ne hukumar ta fuskanta. A don haka hukumar ke sanar da jama’a cewa babu umarnin wani kari a wannan shekarar.”

Ya kara da cewa, NERC zata cigaba da sauke nauyinta kamar yadda dokokinta ska tanadar, kuma zata cigaba da duba lokaci zuwa lokaci a kan kudin da kwastomomi zasu cigaba da biya.

Kamar yadda yace, a duk lokacin da ya kamata a yi duba ko a kara kudin wuta, hukumar sai ta zanta da masu ruwa da tsaki tare da tuntubar duk wadanda abun ya shafa kafin ta yanke hukuncin karshe.

Suraj Fadairo, shugaban hukumar kare hakkin masu amfani da wutar lantarkin ta kasa, ya ce Karin kudin wutar lantarkin ba ita bace tushen matsalar wuta a Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel