Yanzu-yanzu: Kasar Chadi ta janye sojin ta daga yakar Boko Haram

Yanzu-yanzu: Kasar Chadi ta janye sojin ta daga yakar Boko Haram

- Rundunar sojin kasar Chadi mai tallafawa sojin Najeriya wajen yakar Boko Haram sun koma gida

- Har a halin yanzu dai ba a san dalilin janye dakarun da kasar Chadin tayi ba, bayan watannin da suka yi a Najeriya

- A cikin kwanakin baya ne shugabannin kasashen dake da iyaka da tafkin Chadi suka yi taro a Najeriya don hadin guiwar dakaru wajen yakar Boko Haram

Babbar rundunar kasar Chadi wacce ta kunshi a kalla soji 1,200 ta janye daga hadin guiwa na yakar Boko Haram a Najeriya. Mai magana da yawun sojin ne ya sanar da AFP a yau Asabar.

"Dakarunmu ne suka je taimakawa sojin Najeriya a watanni da suka gabata. A halin yanzu sun kammala abinda ya kaisu kuma sun dawo gida," kakakin su Kanal Azem Bermadoa ya sanar da AFP.

"Babu kowanne sojanmu dake Najeriya," ya kara da cewa, ba tare da ya sanar da dalilin da yasa suka janye daga wannan hadin guiwar ba a ranar Juma'a.

DUBA WANNAN: Ma'aikata sun harbe wasu Zakuna uku da suka yi kalaci da gawar wani mutum

Akwai kasashen gefen tafkin Chadi da suka hada guiwa da Najeriya don yakar Boko Haram. Kuma kasar Chadi na daga cikinsu.

Kasar Chadi tayi iyaka da Najeriya ta bangaren Arewa maso Gabas ta cikin jihar Borno.

Sauran kasashen da suka bada gudummawar sojoji tare da hada guiwa da Najeriya domin yakar Boko Haram, sun hada da Kamaru da Nijar.

Idan zamu tuna, a cikin shekarar 2019 ne shugabannin kasashen Afirka dake gefen tafkin Chadi suka yi wani taro a Najeriya tare da shugaba Muhammadu Buhari, domin tattauna yadda za a kara hada karfi da karfe domin kawo karshen aiyukan ta'addanci na Boko Haram.

Ya zuwa yanzu, kasar Chadi bata bayar da dalilai na janye sojojinta daga wannan hadin guiwar ta yakar Boko haram ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel