Tura ta kai bango: Fafaroma ya buge hannun wata mata da ta makalkale shi don kauna

Tura ta kai bango: Fafaroma ya buge hannun wata mata da ta makalkale shi don kauna

Wani hoton Fafaroma Francis yana buge hannun wata mata da ta makalkale shi don kauna ya jawo cece-kuce a kafofin sada zumuntar zamani a kan saurin daukar matakinsa.

Francis ya gaisa da yara kafin ya tsallaka zuwa ginin Waliyyi Peter. A nan ne matar ta koka a kan wani abu kafin ta cafke hannunsa kuma ta sa ya kusan faduwa kasa.

Tsohon mai shekaru 83 wanda kuma shine shugaban majami'ar Katolika yayi taga-taga kamar zai fadi kasa kafin ya buge hannun matar har sau biyu.

Daga nan ne ya cigaba da tafiyarsa da kyar kafin daga baya ya daidaita tare da gujewa kusanci daga baki. Bayan nan ne ya huta tare da cigaba da gaisawa da kananan yara.

DUBA WANNAN: Ba laifi bane murnar sabuwar shekara - Malamin addinin Islama

A nasiharsa ta farkon shekara, shugaban ya fara da jan kunne a kan tozarta mata saboda kowa ya fito ne daga tsatsonsu, lamarin da ya jawo cece-kuce daga ma'abota amfani da kafar sada zumuntar tuwita.

Amma kuma daga baya Fafaroma ya fito ya bada hakuri a kan abinda yayi. "Sau da yawa mu kan rasa hakurinmu", in ji shi.

A ranar Laraba ne Fafaroma Francis ya tabbatar da cewa ya hakurinsa ne yayi karanci da wannan mai kaunar tashi wacce ta makalkale masa hannu a ginin Waliyyi Peter, lamarin da yasa ya buge mata hannu har sau biyu.

"Sau da yawa mu kan rasa hakurinmu. Ta faru dani nima. Ina bada hakuri saboda ban bada misali nagari ba jiya," cewar shugaban majami'ar Katolika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel