Siyasar 2023: Za mu fara farautar sabon dan takarar shugaban kasa a PDP – Shugaba Walid

Siyasar 2023: Za mu fara farautar sabon dan takarar shugaban kasa a PDP – Shugaba Walid

Shugaban majalisar amintattu na jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin ya bayyana cewa nan bada jimawa ba za su fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki da nufin zakulo jajirtaccen dan siyasan da zai daga tutar jam’iyyar a zaben shugaban kasa a kakar zabe na 2023.

Jaridar Punch ta ruwaito Walid ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Kaduna inda yace duk wani dan jam’iyya da ke da ra’ayi, daga kowanni sashi na kasar nan yana da yancin fitowa takarar shugaban kasa.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta raba kayan alheri ga manyan asibitoci 4 a Kaduna

Da aka tambayeshi ko Atiku Abubakar zai iya sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2019, sai Walid Jibrin yace: “Kamar kowanni dan Najeriya, Atiku na da daman fitowa takara, koda yake ba za’a ce Atiku ya gaza a zaben 2019 ba tun da sai da aka fafata a kotu har zuwa kotun koli.

“Don haka idan Atiku yana da burin takara, yana da yancin fitowa, haka zalika sauran jama’a ma nada yancin fitowa, amma kuna ganin Atiku ne kadai ke muradin tsayawa takara?” Inji shi.

Shugaban majalisar amintattu na PDP bai tsaya nan ba, ya cigaba da fadin: “Game da batun dan takarar shugaban kasa, shugabancin jam’iyya tare da hadin gwiwar sauran bangarorin jam’yyar zasu bayyana shirin da suke yi na zaben dan takarar shugabancin kasar nan.

“Ban jin akwai wata matsala game da kyale duk wani mai son taka takarar shugabancin kasa a PDP ya fito, amma gaba dayanmu zamu taru mu yanke hukunci wajen fitar da dan takarar daya kamata.” Inji shi.

A wani labarin kuma, jim kadan bayan fitowarsa daga hannun hukumar DSS, mashawarcin tsohon shugaban kasa Jonathan a kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki ya bayyana cewa a shirye yake ya fara kare kansa a gaban kotu.

Gwamnati na zargin Dasuki da laifin mallakar miyagun makamai ba tare da ka’ida ba, tare da hannu cikin badakalar kudi naira biliyan 35 da kuma satar kudin makamai dala biliyan 2.1 da aka ware domin sayen makamai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel