Takaitaccen tarihin matan shugabannin Najeriya daga 1984 zuwa yanzu

Takaitaccen tarihin matan shugabannin Najeriya daga 1984 zuwa yanzu

A duk lokacin da ka ga namiji cike da izza, kwanciyar hankali da nasarori a rayuwa, zaka ga mace ta gar ice tare da shi. A wannan rubutun an tattara hotuna tare da tarihin mata shuwagabannin kasa Najeriya daga 1984 zuwa yau.

Maryam Babangida (1985-1993)

An haifeta a ranar 1 ga watan Nuwamba 1948 a Asaba, jihar Delta. Tayi karatun sakandirenta a kwalejin sarauniya Amina dake Kaduna, inda ta karasa zuwa cibiyar horarwa ta tarayya a Kaduna. Ta kammala a matsayin sakatariya. Maryam tayi shugabar kungiyar matan sojoji ta Najeriya. Ta rasu ne a California bayan jinyar da tayi ta ciwon daji.

Maryam Abacha (1993-1998)

An haifeta a ranar 4 ga watan Maris 1945. Ita ce mai takabar marigayi tsohon shugaban kasa Sani Abacha. Maryam Abacha na nan a Najeriya ko bayan rasuwar mijinta. Sun haifa ‘ya'ya mata uku da maza bakwai da marigayin. Tana nan a birnin Kano. Itace ta samar da babban asibitin kasa na Abuja.

Jastis Fati Abubakar (1998-1999)

A matsayinta na matar shugaban kasa, ta ki amfani da sunan ‘First Lady’. Tayi amfani da ofishinta yadda ya dace. Ta kirkiro da hukumar kula da ‘yanci tare da habaka mata. Wannan kungiyar ta dade har bayan saukar mijinta don ta bi duk hanyar da ta dace wajen yi mata rijista. Mutane da yawa sunce itace dalili na farko da yasa mijinta ya mika mulki ga zababben shugaban kasa a wancan lokacin.

DUBA WANNAN: Sakon Kirsimeti da Sardauna ya aika wa Kiristocin arewa a 1959

Stella Obasanjo (1999-2005)

Wannan itace matar shugaban kasa na 5 kuma na 12. Mai rajin kare hakkin mat ace da matasa don gobe. Stella kyakyawa ce kuma mai fada aji a wajen mijinta. Yanayin gayu da tsarin rayuwarta daban take da sauran mata. Ta rasu ne lokacin da take da shekaru 59 yayin da ake mata aiki a wani asibiti a kasar Spain.

Turai Yar’adua (2007-2010)

Hajiya Turai Yar’adua ce matar marigayin tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua. Sun yi aure ne tun a 1975. Allah ya yiwa maigidanta rasuwa a lokacin da yake shugabantar Najeriya a 2010. Mace ce da bata cika hayaniya ba, kuma ta kirkiro da cibiyar yakar cutar daji a lokacin da mijinta ke shugabanci.

Patience Jonathan (2010-2015)

Mama Peace daban take a cikinsu. Tun daga yadda take saka sutura zuwa kan kalamanta. Amma kuma aiyukan jin kan ta ba a Najeriya kadai suka tsaya ba, a fadin duniya an san su. Ta karba kambun jinjina daga wata kungiyar taimakon jama’a dake New York a Amurka. Dole ‘yan Najeriya su tuna da ita a kan ‘kisan gillar’ da ta dinga yiwa turanci.

Aisha Buhari (2015- yau)

Itace uwargidan Muhammadu Buhari. Ta kasance daya daga cikin matan da suke tsananin fitowa su sanar da ra’ayinsu a kafafen sada zumuntar zamani kuma da dukkan gaskiyarta. Gaskiyarta ce ta sa maigidanta ya ce huruminta na 'madafi da dayan dakin’. Yanayin kayan da take sanyawa wani abu ne na daban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel