Shekau ya saki sakon Kirsimeti a cikin sabon faifan sautin murya

Shekau ya saki sakon Kirsimeti a cikin sabon faifan sautin murya

Kamar yadda Ahmad Salkida mai bada rahoton aiyukan 'yan Boko Haram tun tsakiyar 2006 ya bayyana, ya ce Abubakar Shekau ya saki wani sakon Kirsimeti na murya.A sakon ne yake bayyana cewa "Yesu ba dan Allah bane."

Shekau ya kara da jaddada barazanarsa ga Kiristoci da Musulmai masu goyon bayan al'adun da ba na musulunci ba. Ya tabbatar da cewa yana jin wa'azi daga gidajen rediyo daban-daban.

Majiyoyi masu yawa sun bayyana cewa Abubakar Shekau da ISWAP sun saki faya-fayan bidiyo daban-daban a jiya ranar bikin Kirsimeti. Bayyanannen abu ne cewa kungiyoyin 'yan ta'addan na amfani da ranar bikin Kirsimetin ne don mika sakonninsu.

Wannan kuwa ya zamo kamar a kan gaba ne don bangarorin biyun a farkon makon nan sun yi karon batta inda wasu daga cikinsu suka jigata.

Hukumomi a Najeriya sun yadda cewa an kashe Shekau a 2009 a yayin wani gumurzu da aka yi tsakanin dakarun Najeriya da mayakan Boko Haram.

DUBA WANNAN: Kano: Gwamnati ta rufe gidan 'Mayu'

Wannan hasashen ya shafe ne a watan Yuli na 2010 bayan da Shekau ya bayyana a sabon faifan bidiyo yana jaddada zama shugaban kungiyar.

Ba sau daya ba ko biyu ba, aka ruwaito cewa Shekau ya mutu; lamarin da yasa ake zargin ko ba mutum daya bane ke amfani da sunan.

A watan Maris na 2015 ne Shekau ya yi mubaya'a ga Shugaban kungiyar ISIL, Abu Bakr al-Baghdadi. Shekau mabiyin bangaren Salaf ne. An kwatanta cewa yana da wata kwalwalwa mai haddace abu a duk lokacin da ya ganshi.

Wannan sakon muryar kuwa wata hujja ce da ke kara tabbatar da cewa Shekau na nan a raye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel