Gwamnoni 10 da suka mallaki makudan kudi da adadinsu
Idan aka yi maganar arziki, ballantana wanda ya shafi ‘yan siyasa, wasu kan fara dangantashi da almubazzaranci. Amma ba koda yaushe hakan yake zama gaskiya ba. Wasu daga cikin gwamnonin nan 10, sun tara arzikinsu ne ta hanyar fafutukarsu tare da kasuwancinsu.
Mai karatu ya sani, da yawa daga cikin gwamnonin nan basu dade da hawa mulki ba. Ga jerin gwamnoni 10 na Najeriya masu arziki a shekarar 2019.
1. Gwamna Sani Bello (sama da $1billion)
Abubakar Sani bello gwamnan jihar Neja ne wanda ya hau mulki a 2019. Yafi kowanne gwamna a Najeriya dukiya. Wannan gwamnan sunansa ya bayyana a jerin manyan masu kudi da Forbes ta bayyana. Ya tara dukiyarsa ne tun kafin ya hau shugabancin jihar Neja.
2. Gwamna Nyeson Wike (sama da $550 million)
Gwamna Ezenwo Nyeson Wike shine gwamnan jihar Ribas a Najeriya. Shine gwamna na biyu a wannan jerin. Gwamna ne a karkashin jam’iyyar PDP. Ya samu soyayyar jama’ar jiharsa ne sakamakon aikinsa tukuru. Lauya ne kuma dan siyasa ne.
3. Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai (Sama da $400 million)
Malam shine gwamna na uku a wannan jerin. Gwamnan ya rike ministan birnin tarayya . An gano cewa, ya tara dukiyarsa ne tun yana da kananan shekaru.
4. Gwamna Dapo Abiodun (Sama da $314 million)
Gwamnan jihar Ogun ne da kwanan nan ya samu nasara a kotun koli. Jiharsa na daya daga cikin manyan jihohin Najeriya. Shine mamallakin kamfani mai da iskar gas na Heydon. Gwamnan ya kasance hamshakin mai arziki tun kafin ya hau shugabancin jihar Ogun.
DUBA WANNAN: Ba laifi bane don 'miyagu' sun kewaye Buhari - Fadar shugaban kasa
5. Gwamna Willie Obiano ($300 million)
Gwamnan jihar Anambra ne a karkashin jam’iyyar APGA. Gwamnan ya kasance hamshakin mai kudi tun a lokacin da yake samartaka. Ya fara aiki ne da First Bank kafin ya koma siyasa.
6. Gwamna Godwin Obaseki ( $225 million)
Gwamnan jihar Edo din ya kasance shugaban Afrinvest har zuwa watan Yuni na 2016. Ya yi aiki a kamfanoni daban-daban da suka hada da tsaro da sauran aiyukan da suka mayar dashi hamshakin mai arziki.
7. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ($27 million)
Shine na bakwai a wannan jerin kuma gwamnan jihar Sokoto a Najeriya. Gwamnan a karkashin jam’iyyar PDP din yayi kakakin majalisar wakilan Najeriya. Ya kuma tara dukiyar da ta kai $27 million.
8. Gwamna Yahaya Bello ($5.6 million)
Gwamnan jihar Kogi din ya zarce mulkin jihar a zaben da aka yi kwanakin nan. Gwamna a karkashin jam’iyyar APC din ya samu dukiyarsa ne tun yana matashi.
9. Gwamna Bala Mohammed
Ya yi ministan babban birnin tarayya ta Abuja . Ya karanci turanci a jami’ar Maiduguri. Gwamnan ya tara dukiyar da ta kai $2.5 million.
10. Gwamna Samuel Ortom ($2.5 miilion)
Wannan ne gwamna na 10 a wannan jerin. Gwamnan jihar Benuwe din ya samu kambu tare da lambobin yabo a siyasa. Ya kirkiri gidauniyar tallafi ta Oracle Business Limited Foundation, wanda yake amfani da ita wajen tallafawa marasa karfi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng