Na fasa auren: Fusataccen ango ya tafi ya bar amarya ranar daurin aure (Bidiyo)

Na fasa auren: Fusataccen ango ya tafi ya bar amarya ranar daurin aure (Bidiyo)

Wani bidiyon ango a Najeriya ya yawaita a kafafen sada zumuntar zamani. Bidiyon ya jawo cece-kuce sakamakon abinda ya faru.

Kamar yadda jaridar The Watch News ta wallafa, angon ya bayyana a bidiyon yana tafiya amma mutane tare da amaryar suna rokonsa.

Angon na ta tirjiya tare da bayyana cewa, ya fasa auren tare da wucewa don barin amaryar.

Kamar yadda wakilin jaridar The Watch News ta ruwaito, angon ya bayyana cewa amaryar tana cin amanarsa ne amma bai taba sani ba sai a ranar. Ya ce, a lokacin da fasto ya ke gab da daura musu aure, sai ya tambaya ko akwai wanda bai amince da wadannan mutanen su zama ma'aurata ba, sai wani mutumi ya fito tare da bayyana cewa suna da wata alakar sirri tsakaninsa da amaryar.

DUBA WANNAN: Ba laifi bane don 'miyagu' sun kewaye Buhari - Fadar shugaban kasa

Hakan kuwa ya harzuka angon kuma ya jawo yanke wannan hukuncin na fasa auren.

Daga bakin fusataccen angon: "a yayin da fasto yake gab da daura auren, sai ya waiwaya tare da tambayar wanda bai gamsu da mu zama mata da miji ba. A take wani mutum ya fito tare da sanar da jama'a cewa suna da wata alakar sirri tsakaninsu da amaryata. A take kuwa na bar cocin tare da hakura da auren."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel