Tirkashi: Daga kai 'yarta Fasto ya cire mata aljanu, sai ta kama shi yana lalata da ita
- A wani kauye mai suna Obosi ne na jihar Anambra wata mahaifiya ta kai karar wani faston da ake kira da 'Agudo Jesus'
- Mahaifiyar ta ce, ya zo ya karba matashiyar budurwar 'yarta da zummar mata addu'a don cire mata miyagun shaidanu amma sai ya bige da sha'aninshi da ita
- Faston ya samu mahaifiyar ne tare da sanar da ita cewa 'yarta zata zama mashahuriyar mai kudi amma akwai shaidanun aljanu dabaibaye da ita
A wani kauye mai suna Obosi ne na jihar Anambra jami'an 'yan sanda suka kama wani faston majami'ar Mountain of fire ministries mai suna Chukwudi Chukwumezie wanda aka fi sani da 'Agudo Jesus' da laifin lalata da wata matashiyar budurwa.
An bankado cewa, hakan ba shine na farko ba da wannan faston ke aikata irin wannan mummunar dabi'ar.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya bayyana cewa, a ranar 24 ga watan Satumba ne mahaifiyar budurwar ta garzayo don mika kokenta a kan yadda Agudo Jesus yayi lalata da 'yar ta.
Mahaifiyar budurwar ta shaida cewa, wani fasto ya zo gidanta inda ya bayyana mata cewa, wannan budurwa zata zama babbar attajira, sai dai akwai shaidanun aljanu da suke dabaibaye da ita. Hakan kuwa zai iya zama cikas ga cikar wannan lamari.
KU KARANTA: Zan bi diddigin kisan matashi Mus'ab har sai gaskiya ta yi halinta - Sheikh Isah Ali Pantami
Ya kara da bayyana cewa, anyi mishi wahayi da ya dinga biya mata kudin makaranta.
"Daga nan sai ta mika mishi wannan matashiyar budurwa. Shi kuwa gogan naka sai ya dinga lalata da ita kuma yana mata addu'o'in karya. Yarinyar ta bayyana cewa, takan bude ido ne ta ganshi a kan gado tare da ita."
Sai dai Agudo Jesus ya musanta aukuwar lamarin, ya ce sharri ne kawai aka yi mishi.
A karshe, Mohammed yace sakamakon gwajin likita ya nuna tabbas an yi lalata da matashiyar budurwa. Hakazalika, an samu shaidu kuma daga dakin otal din da Agudo ya dinga lalata da ita.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng