Dalilina na zaben 'yan APC a cikin sabbin kwamishinoni - gwamna Matawalle

Dalilina na zaben 'yan APC a cikin sabbin kwamishinoni - gwamna Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya kare kansa a kan zabar mambobin jam'iyyar APC a cikin sunayen sabbin kwamishinonin da ya ke son nada wa.

A ranar Talata ne gwamna Matawalle ya aika da sunaye mutane 19 da yake son bawa mukamin kwamishina zuwa ga majalisar dokokin jihar Zamfara, kuma a cikinsu akwai mambobin jm'iyyar APC.

Da yake bayyana dalilinsa na saka sunayen mambobin jam'iyyar APC a cikin kunshin kwamishinonin, Matawalle ya ce yin hakan na daga cikin manufarsa na kafa gwamnati ta kowa da kowa.

"Ba wani abin mamaki bane, saboda wannan ba shine karo na farko ba. Irin hakan ta faru a wurare da dama," a cewar gwamna Matawalle ta bakin darekransa na yada labarai, Alhaji Yusuf Idris.

Da yake karanta sunayen mutane 19 da gwamnan ya aika, kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Nasiru Magarya, ya lissafa su kamar haka; Alhaji Sulaiman Tunau, Alhaji Aminu Sulaiman, Abdulkadir Buhari Gora, Jinaidu Muhammad, Muhammad Sadiq Maiturare, Zainab Lawal Gummi, Jamilu Aliyu, Dr Nura Isah and Rabiu Garba.

Ragowar sun hada da wurin tsohon ministan kudi, Sufyanu Bashir Yuguda, Ibrahim Jibo Magayaki, Yahaya Chado Gora, Yahaya Muhammad Kanoma, Sheik Tukur Sani Jangebe, Ibrahim Isah Mayana, Abubakar Abdullahi Tsafe, Barr Nura Ibrahim Zarumi, Bilyaminu Yusuf Shinkafi da Abubakar Muhammad.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel