Abubuwa 5 game da dokar takaita amfani da kafafen sadarwar zamani

Abubuwa 5 game da dokar takaita amfani da kafafen sadarwar zamani

Yan Najeriya sun ciri tuta wajen amfani da shafukan sadarwar zamani inda kiyasin alkalumma ya nuna akwai yan Najeriya miliyan 111.6 dake amfani da yanar gizo a nahiyar Afirka, wanda hakan yasa yan Najeriya suka yi zarra a wannan fanni.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, jama’a da dama na kokawa game da yadda wasu yan Najeriya ke amfani da shafukan sadarwar zamani kamarsu Facebook, Twitter, Instagram, WhatsApp da sauransu, duba da yadda ake samun yawaitan cin mutunci da watsa labarun karya.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya tashi daga Daura, ya tsaya a garin Kaduna

Ba komai bane ya janyo hakan face daman da kowa ke da shin a tofa albarkacin bakinsa a cikin lamurran da suka shafe shi da ma wanda basu shafe shi ba kai tsaye daga wayarsa yana kwance a cikin daki ba tare da wani wahala ba.

Wannan yasa Sanata Mohammed Sani Musa na jahar Neja ya gabatar da kudurin kayyade amfani da kafafen sadarwar zamani a ranar 5 ga watan Nuwamba mai taken “Kudurin kariya daga labarun karya a shafukan yanar gizo 2019”

Sanata Musa yace babban manufar wannan kuduri shi ne wayar da kan masu amfani da kafafen sadarwar zamani game da muhimmancin sa kuma yadda ya kamata su yi amfani dasu, ba wai ana kokarin hana jama’a tofa albarkacin bakunansu bane.

Ga dai wasu muhimman abubuwa da wannan kudurin doka ta kunsa kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito;

- Manufar kudurin shi ne tsaftace yadda ake amfani da kafafen sadarwar zamani

- Duk wanda aka kama da laifin watsa labaran karya za’a ci shi taran N150,000 ko daurin wata 3 a kurkuku

- Duk kamfanin da bata dakatar da labaran karya ba bayan hukuma ta sanar da ita cewa labarin karya ne za’a ci ta tara daga naira miliyan 5 zuwa 10

- A shekarar 2015 ma an gabatar da irin wannan kuduri a majalisa

- A ranar 26 ga watan Yuni na 2018 gwamnati ta sake mika kudurin ga majalisa

Sai dai yan Najeriya da dama sun yi Allah wadai da wannan kuduri, inda wasu ke ganin wani sabon salo ne na yi ma yan Najeriya karfa karfa game da abinda ya shafi yancinsu na fadar ra’ayinsu ba tare da tsoro ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel