Pantami ya samu lambar yabo

Pantami ya samu lambar yabo

Kokarin dawo da martabar aikin gwamnati ta yadda shuwagabanni zasu isar da aiyukansu a bayyane, cikin sauki kuma babu boye-boye bai tashi a banza ba. An zabi ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, shi kadai, don karramasa sakamakon jajircewarsa, maida hankali da kokarinsa.

An bada lambar yabon ne ga ministan yayin bikin bada lambar yabo ta fasahar yada labarai ta kasa da aka yi a Legas. Bikin ya samu shugabancin ministan, wanda babban daraktan kamfanin sadarwar tauraron dan Adam, Dr Abimbola Alale ya wakilta.

Idan muka duba irin tsokacin da ke fitowa daga bakin mutane, wannan ba abun mamaki bane. Bayan nadashi a matsayin ministan sadarwan Najeriya, Dr Pantami ya fifita aiyukan cigaban kasa fiye da komai da ke gabansa.

Sabon ministan, ya gayyaci duk wasu bangarorin da ke karkashin kulawar ma'aikatarsa, tare da bayyana musu umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, do tabbatar da duk cibiyoyin gwamnati sun isar da aiyukan da aka sasu ga 'yan Najeriya.

Tun a shekarar 2001, matsalar rijistar layikan wayoyi ta kasance abinda ke hada kanun labarai, tare da tattaunawa a kafafen sada zumunta zamani. Kokarin shawo kan matsalar a siyasance babu ita ko kadan.

DUBA WANNAN: Nasarar APC: Yahaya Bello babban 'dodo' ne - Oshimhole

A kasa da kwanaki 40 da minstan ya fara shugabantar masana'antarsa, ya shawo kan wannan kalubalen kuma ya tabbatar da cewa, babu layin waya da ake amfani dashi a yanzu babu rijista.

Wannan rijistar ta zamo babban makami wajen tsaron kasa, da kuma samar da hanya mafi sauki ga cibiyoyin tsaro wajen ganowa tare da binciko duk wani ta'addanci da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, damfarar kudi, ta'addanci da sauran laifukan da ake iya aikatawa da layikan waya.

Wannan ne karo na farko a tarihin Najeriya da koken 'yan Najeriya ko kamfanonin sadarwa ke kaiwa gwamnati. Ba kaiwa gwamnati kadai ba, ana daukar matakin gaggawa da suke kawo aiyuka nagari kuma masu nagarta.

Ba abun mamaki bane da mai girma shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya nemi shawarar kwararren ministan wajen lamurran da suka shafi tsaron kasa ba.

Ministan ya shawo kan matsalar rashawa da ta cika hukumar NIPOST, ta hanyar hana biyan duk wata huldarsu sai ta banki. Ba kuma abun mamaki bane da karamin ministan kwadago, Festus Keyamo, ya kwatanta abokin aikin nasa da mai gaskiya kuma hazikin mutum wanda ke da daraja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel