Sojojin Najeriya sun tarwatsa gungun mayakan Boko Haram, sun kwace makamai

Sojojin Najeriya sun tarwatsa gungun mayakan Boko Haram, sun kwace makamai

Dakarun rundunar Sojojin Najeriya na bataliya ta 153 dake aikin tabbatar da tsaro a yankin New Marte dake cikin karamar hukumar Dikwa na jahar Borno sun yi karan batta da mayakan kungiyar yan ta’adda na Boko Haram, inda suka yi kuli kulin kubura dasu, suka ranta ana kare tare da zubar da makamansu.

Kaakakin rundunar Soji, Kanal Aminu Iliyasu ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba inda yace an yi wannan bata kashi ne a ranar Litinin, inda Sojoji suka samu nasarar kashe mayakan Boko Haram da dama.

KU KARANTA: Wuta ta kona gawarwakin mutane 12 a babban asibitin koyarwa

A cewar Aminu, kaikayi ne ya koma kan mashekiya, sakamakon yan ta’addan ne suka shirya ma Sojoji kwantan bauna a daidai kauyen Ala dake kusa da sabuwar Marte. “Amma da yake Sojojinmu suna da kwarewa, sai reshe ta juye da mujiya, inda suka mayar da wuta, suka yi ma yan ta’addan rakiyar kura

“Yan ta’adda da dama sun mutu a wannan hari, sa’annan wasu sun tsere sun zubar da makamansu, amma duk da haka Sojojinmu basu tsaya nan ba, sai da suka bi sawunsu domin gamawa da su.” Inji shi.

Kanal Aminu yace daga cikin abubuwan da suka gano akwai: Manyan motoci masu girke da bindigu guda 2, alburusai 2,080, bindigar AK 47 guda 3, babur daya, kayan sawa, kayan abinci, karafan gyaran motoci da dai sauransu.

Daga karshe Aminu ya bada tabbacin yan ta’adda da dama sun tsere da rauni daban daban a wannan batakashi, sa’annan yace Sojoji na cigaba da kwato wuraren da yan ta’addan suka mamaye wanda hakan ya hana musu sakat.

A nasa jawabin, babban hafsan sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya jinjina ma dakarun Sojin Najeriya bisa wannan nasara da suka samu, inda ya nanata manufar rundunar Sojan kasa wajen gudanar da aikinta cikin kwarewa da kuma kare martabar Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel