Manyan masu kudin duniya 5 da basu kammala sakandire ba

Manyan masu kudin duniya 5 da basu kammala sakandire ba

Akwai labaran na sanannun mutane da suka bar kwaleji kuma suka zama manyan masu kudi amma kalilan ne zaka samu sun bar sakandire kuma suka samu arziki mai tarin yawa a duniya.

Manyan masu kudi na duniya da basu kammala sakandire ba kuma suka samu dukiya a duniya sun kasance a masana'antun kyale-kyale, fasaha da waka. Ga kadan daga cikin wadanda Ubangiji ya tarfa wa garinsu nono duk da basu kammala karatun sakandire ba.

1. Jay-Z: Mashahurin mawakin gambara ne kuma bai kammala karatun sakandire ba. Mawakin gambarar ya kasance mai bayyanawa mutane amfanin ilimi.

2. Richard Branson: Daya daga cikin masu kudin duniya ne da ya bar makaranta tun yana da shekaru 16 a duniya. Shi ne mamallakin Virgin Group. Jim kadan bayan barin makarantar da yayi, ya bude kamfaninsa na farko wanda shine ya zamo 'Virgin Records' a yanzu.

'Yan kasuwa irin Richard Branson da mawakin gambara Jay-Z suna da kamanceceniya ta waje daya: Dukkansu manyan masu kudi ne kuma basu kammala karatun sakandire ba.

Amma ba su kadai bane masu kudi a duniya da basu kammala sakandire ba. A yayin da wasu sanannun mutanen da suka bar jami'a suka zama manyan masu kudi, kamar su Mark Zuckerberg da Bill Gates, ba a cika samun wadanda basu gama sakandire ba sun kai irin matakinsu.

DUBA WANNAN: Mata da miji sun gano cewa ubansu daya bayan shekaru 24 da aure

3. Zhou Qunfei: Ta bar makarantar sakandire tana da shekaru 16 a duniya inda ta fada aiki a wani kamfanin gilasan agogo. Tana samun zuwa ajin lissafin kudi da dare, daga nan ta tara 2,000HKS wanda yayi daidai da kusan dala 2,500. Ta bude kamfanin gilashin agogo nata na kanta inda ta jagorance shi da 'yan uwanta.

A halin yanzu itace mai kamfanin gilashin da ke samarwa da kamfanin Apple, Samsung da Tesla gilasan kayayyakin da suke hadawa.

4. Amancio Ortega: Ya bar makaranta ne yana da shekaru 14 kacal a duniya inda ya zama dan aiken wasu masu shaguna. Bayan shekaru, Ortega ya samar da kamfanin sarkar Zara a kasarshi ta Spain. Kamfanin ya cigaba da bunkasa. A yau shine mafi arziki na biyu a Turai.

5. Francois Pinault: Shine ya samar da kungiyar Kering. Ya bar makaranta yana da shekaru 11 a duniya inda ya koma aiki a kamfanin katakon mahaifinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel