Karfin arziki: Attajiran kasar Qatar zasu gina makarantu da Asibitoci a Najeriya

Karfin arziki: Attajiran kasar Qatar zasu gina makarantu da Asibitoci a Najeriya

Wata kungiya mai zaman kanta mallakin wasu attajiran kasar Qatar mai suna Qatar Charitable Organization ta yi alkawarin sake gina makarantu da Asibitocin da kungiyar yan ta’adda ta Boko Haram ta lalata a jahar Yobe.

Jaridar The Sun ta ruwaito kungiyar za ta gudanar da wannan aiki ne a kananan hukumomi 17 da rikicin Boko Haram ya shafa a jahar, kamar yadda shugaban kungiyar, Hamdi Elsayed ya tabbatar a yayin zamansu da gwamnan jahar Yobe.

KU KARANTA: Tsunstun daya kira ruwa: Malamin daya zakke ma yarinya ya gamu da daurin shekaru 60

Majiyar Legita.ng ta ruwaito a jawabinsa, Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana godiyarsa ga kungiyar bisa wannan aikin sa kai da ta yi niyya, sa’annan yace jahar Yobe na farfadowa sosai daga hare haren Boko Haram.

“A yanzu zaman lafiya na dawowa jahar Yobe, akwai tsaro a Yobe sosai, ina tabbatar muku mun samar da filayen da za’a gudanar da wannan ayyuka, kuma zamu yi aiki tare daku don ganin an kammala wadannan ayyukan cikin nasara domin jama’anmu su amfana.” Inji shi.

Shi ma a nasa jawabin, Hamdi ya bayyana cewa ba zai fadi asalin adadin kudin da zasu kashe ba, amma yace yana sa ran zasu kashe kimanin naira miliyan 100 a kan ayyukan zuwa shekarar 2020.

“Zamu je Yobe nan bada jimawa ba don ganin filayen da kuka ware, sa’annan mu kai ma uwar kungiyarmu rahoto a Qatar, baya ga ginin makarantu da asibitoci zamu gina famfon tuka tuka guda 17 da famfon injina guda 20.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel