Tsunstun daya kira ruwa: Malamin daya zakke ma yarinya ya gamu da daurin shekaru 60

Tsunstun daya kira ruwa: Malamin daya zakke ma yarinya ya gamu da daurin shekaru 60

Kowa ya debo da zafi bakinsa, kamar yadda masu iya magana suke cewa, anan ma wata kotun hukunta laifukan da suka danganci fyade ne ta yanke ma wani magidanci mai shekaru 47 hukuncin daurin shekaru 60 a kurkuku.

Jaridar The Nation ta ruwaito mutumin mai suna Adegboyega Adenekan ya kasance babban malami ne dake kula da wata makarantar firamari a jahar Legas, da haka ne ya lallaba ya yi ma yarinya yar shekara 2 fayde.

KU KARANTA: Kungiyar Boko Haram ta samu karin mayaka 2000 daga ISIS – Shugaban kasar Rasha

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun, mai sharia Sybil Nwala ya bayyana cewa ya kama Adenekan da laifin aikata fyade ga wannan yarinya, wanda dama itace kadai tuhuma daya tilo da masu kara suke yi masa.

Daga karshe Alkalin ya yanke hukuncin daurin shekaru 60 ga Adenekan a gidan yari tare da horo mai tsanani.

A wani labarin kuma, jami’ar jahar Kaduna ta dakatar da wani jami’inta mai suna Bala Umar wanda ake kira da suna A.B Umar biyo bayan tuhumarsa da wata daliba ta yin a cewa ya taba nemanta da nufin lalata lokacin da yake jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Mahukuntan jami’an KASU sun kafa wata kwamiti da zata yi duba ga tuhumar da ake yi ma AB, sa’annan sun kafa wata kwamiti na daban da zata bincike aukuwar ire iren miyagun ayyukan nan a cikin jami’ar ta KASU.

Ita dai wannan daliba da ba’a bayyana sunanta ba ta bayyana cewa jami’ar ABU ta sallami AB Umar ne a kan laifin neman lalata da dalibai mata, don haka take ganin bai kamata ya yi aiki a kowanne makaranta ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel