Karshen duniya: Asirin wani mutumi ya tonu bayan an kama shi ya kashe dan cikinsa saboda tsananin luwadi da yake da shi ta karfin tsiya

Karshen duniya: Asirin wani mutumi ya tonu bayan an kama shi ya kashe dan cikinsa saboda tsananin luwadi da yake da shi ta karfin tsiya

- Asirin wani mutumi ya tonu bayan an kama shi ya kashe dan cikinsa saboda tsananin luwadi da yake da shi ta karfin tsiya

- An gano hakan ne bayan an garzaya da yaron asibiti, inda aka gano cewa duburar sa ta lalace baki daya

- Yanzu haka dai za a gurfanar da mutumin a gaban kotu domin yanke masa hukuncin kisa akan abinda ya aikata

Asirin wani mutumi dan shekara 25 a duniya mai suna Muchiri Derick ya tonu bayan 'yan sandan kasar Kenya sun kama shi da laifin yiwa dan shi mai watanni shida a duniya fyade har ta kai ga ya mutu.

Kwamishinan 'yan sanda na Tharaka-Nithi, Ms Opwora Beverly ta sanar da hakan a jiya Laraba 23 ga watan Oktobar nan, a lokacin da take magana da manema labarai a ofishin ta.

Ta bayyana cewa jaririn ya mutu ne bayan an garzaya da shi asibitin Mutunguni, inda iyayen nashi suka dauke shi domin duba lafiyar shi a safiyar ranar Litinin.

Sai dai likitoci sun bayyana cewa duburar jaririn ta lalac baki daya, hakan ya sanya suka sanar da 'yan sanda halin da ake ciki.

KU KARANTA: Kano ko da me ka zo an fika: An bude gidan sayar da abincin Naira 30 a jihar Kano

Daga baya kuma an gano cewa mahaifin jaririn ne yake luwadi da shi da har lamarin ya kai ga wannan matsayi.

A cewar kwamishinar 'yan sandan, wanda ake tuhumar dama can cikakken dan shaye-shaye ne, wanda ya sha taimakawa jami'an 'yan sanda wajen gabatar da binciken su.

A karshe ta bayyana cewa za a gurfanar da shi a gaban kotu domin a yanke masa hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel