Allah ya yiwa Muhammadu Dan Madami, Sa’in Katagum rasuwa

Allah ya yiwa Muhammadu Dan Madami, Sa’in Katagum rasuwa

Alhaji Muhammadu Dan Madami, Sa’in Katagum wanda yake daya daga cikin ‘yan majalisar masarautar Katagum ya rasu yana da shekaru 85 a duniya.

Marigayi Sa’in Katagum tsohon jami’in ‘yan sanda ne wanda ya kai matakin DIG kafin ya yi murabaus. Ya kuma rasu ya bar babban wansa, Alhaji Dansidi wato Kilishin Katagum, mata uku da yara 27.

KU KARANTA:Fintiri ya zabi dandan Atiku da wasu mutum 22 a matsayin kwamishinoninsa

Daga cikin yaransa akwai Alhaji Nura Danmadami wanda ke aiki da hukumar DMO da kuma wani babban jami’in kwastam Ahmed Danmadami. Kamar yadda rahotanni suka nuna ya rasu bayan ya dade yana jinya.

Babban limamin fadar Sarkin Katagum, Mallam Ayuba ne ya jagoranci yi masa sallar jana’iza, inda ya roki Allah ya gafarta masa kurakurensa ya kuma sa al-jannah ce makomarsa.

Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Alhaji Yayale Ahmed, mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda a shiyya ta 12 wanda ya wakilci Sufeto janar da kuma manya-manyan ma’aikatan gwamnati sun halarci jana’izar.

Wani dan uwan mamacin, Alhaji Baba Sa’idu Toro ya shaidawa manema labarai cewa a ranar 31 ga watan Disemba, 1983 ne marigayin ya yi murabus daga aikin dan sanda yana matsayin DIG.

Tun daga lokacin ya dukufa wurin yiwa al’umma hidima tare da bin koyarwar addinin musulunci. Danmadi mutum ne mai matukar son taimakon jama’a, kamar yadda Sa’idu Toro ya fadi.

https://www.dailytrust.com.ng/sain-katagum-dies-at-85.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel