Dubu ta cika: Katon gardi dake shigar mata yana cutar samari ya shiga hannu

Dubu ta cika: Katon gardi dake shigar mata yana cutar samari ya shiga hannu

- Asirin wani katon gardi ya tonu, bayan an kamashi yana shigar mata yana damfarar maza

- An bayyana cewa saurayin ya kware matuka wajen shigar mata ya dinga yaudarar maza suna bashi kudi

- Asirin sa ya tonu ne bayan ya yaudari wani saurayi na tsawon shekara uku suna soyayya ba tare da saurayin ya gane ba, sai da suka zo maganar aure

Wani katon saurayi da ya kware wajen shigar mata yana cutar samari ya gamu da gamonsa bayan ya afka wajen da asirinsa ya tonu bayan ya gama cutar mutane masu tarin yawa.

Asirin wannan katon gardi ya tonu ne bayan sun kulla wata soyayya mai karfi da wani saurayi inda har maganar ta kai ga sun fara zancen aure, fara maganar shirin auren na su keda wuya gaskiya ta fara fitowa.

Bayan sun shafe sama da shekara uku rigis suna rangada soyayya, saurayin dake soyayya da dan daudun ya nemi suyi aure, inda ya nemi su fara gabatar da al'adu irin na aure kamar yadda al'adar gargajiya ta tanada.

KU KARANTA: Babbar magana: Yadda Malami na ya dinga kama mini nono yana neman lalata dani a cikin ofis din sa - Daliba ta tona asirin bunsurun malami

Sai dai da fara wannan maganar aka gane lallai wannan mutumi ba mace ba ce katon gardi ne ya kware wajen damfara da yaudarar samari yana karbe musu kudi.

Hakan ya sa aka bukaci samari da su dinga gabatar da kwakkwaran bincike kafin su kai ga maganar aure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel