NYSC za ta gina gidan rediyo na miliyoyin kudi a Abuja

NYSC za ta gina gidan rediyo na miliyoyin kudi a Abuja

Hukuma mai kula da yiwa kasa hidima ta NYSC ta ce za ta gina wani katafaren gidan rediyo a babban birnin tarayya Abuja zuwa shekara mai zuwa.

Hukumar ta ce naira miliyan 50 take tsammanin za ta kashe domin gudanar da wannan aikin. Kamar yadda wakilin jaridar Punch ya bamu labari, gidan rediyon zai ta’allaka ne akan shirye-shiryen hukumar na kasar gaba daya.

KU KARANTA:Mata ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta bayan sun shekara 12 tare

Haka kuma za a rinka amsa tambayoyi da suka shafi ayyukan NYSC. Wata majiyar ta sanar damu cewa, gidan rediyon zai rinka bayyana bukanta masu yiwa kasa hidima dake zaune a garuruwan dake fama da matsalolin tsaro.

Shugaban hukumar NYSC, Birgediya janar Shuaibu Ibrahim ya fadi da bakinsa a ranar 3 ga watan Oktoba, 2019 cewa an ba shi izinin bude sabon gidan rediyon FM a Abuja.

Rahotanni da dama sun bayyana mana cewa, hukumar ta ware naira miliyan 50 a matsayin kudin da zata gina gidan rediyon da su. Kuma hukumar za ta ciri kudin ne daga cikin kasafin kudinta na shekarar 2020.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, wata mata mai shekaru 40 a duniya ta nemi a rabata da mijinta saboda damu da ita ba ballanta yaranta.

Matar ta shaidawa kotun gargajiya ta Ado-Ekiti cewa sun shekara 12 suna tare da ita da mijin nata, kuma yaransu biyu a yanzu haka. Amma kuma banda duka da zagi ba abinda mijin ke yi mata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel