Mata ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta bayan sun shekara 12 tare

Mata ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta bayan sun shekara 12 tare

Wata mata mai suna, Motunrayo Ajayi yar shekara 40 a duniya, ta kai karar mijinta Taiwo Ajayi kotun gargajita ta Ado-Ekiti inda ta nemi a raba aurensa saboda rashin kulawar da bata samu.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN, sun ruwaito cewa matar da mijin nata sun kasance ma’aurata tsawon shekara 12 kenan yanzu inda Allah ya albarkace su da samun ‘ya’ya biyu.

Dalilin matar kuwa na neman a raba aurensu shi ne bai damu da ita da ‘ya’yanta ba, kamar yadda majiyoyi da dama suka ruwaito mana. Daga duka sai zagi da hantara ke shiga tsakaninsu a cewar matar.

KU KARANTA:Gaskiya matar Davido tayi sa’a da mahaifiyarsa ba ta raye, saboda uwar miji ke sa a saki mace – Jaruma mai sayar da maganin maza

Motunrayo ta ce: “Tun shekaru biyu da suka wuce na bar gidan mijina. Abinda yake yi min ne ya isheni da zarar na tambayi kudin makarantar yara ko kuma na abinci sai ya rufe ni da duka.

“Sam bai damu da iyalinsa ba, musamman yaransa. Saboda haka da na ga abinshi ya yi yawa sai na kwashe kayana na bar masa gidan. Amma duk da haka yana biyo ni wurin da na koma yana lakada min dan banzan duka.” Inji matar.

Bayan ta gama zayyanawa kotun labarinta, Motunrayo ta roki a raba aurensu saboda ita bata shirya mutuwa ba a yanzu, kamar yadda ta fadi. Haka kuma tana so kotu ta bata damar rike yaranta.

Sai dai kuma, a nashi bangaren, mijin nata Ajayi mai shekaru 48 ya karyata abinda matarsa ta fadi. Inda ya ce shi bai dukanta kuma shekara daya da ta wuce ne ta bar gidansa.

Mai shari’ar kotun, Mrs Olayinka Akomolede ta dage sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel