An bada labari game da rayuwar tsohon Shugaban kasan Najeriya cikin wani sabon fim

An bada labari game da rayuwar tsohon Shugaban kasan Najeriya cikin wani sabon fim

An bada labarin rayuwar tsohon Shugaban kasan Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida wanda aka fi sani da IBB cikin wani fim din turanci mai suna ‘Badamosi: Potrait of a General’.

Fim din wanda ya samu rubutu da kuma umarni daga wurin shahararren mai rubuta fina-finai, Obi Emelonye ya tabo abubuwa da dama game da rayuwar IBB tun daga yarintarsa har zuwa lokacin da ya zamo Shugaban Najeriya.

KU KARANTA:Uba ya dankarawa diyarsa cikin shege a jihar Gombe

Haka zalika, marubucin ya tabo abubuwa daban-daban dangane da rayuwar tsohon Shugaban kasan. Babangida ya kasance bisa kujerar shugabancin Najeriya daga ranar 27 ga watan Agusta, 1985 zuwa 26 ga watan Agusta, 1993.

Kafin zamansa Shugaban kasa ya rike mukamin Hafsun sojin kasa na Najeriya daga watan Janairun 1984 zuwa watan Agustan 1985. Babangida ya taka rawar gani a cikin jerin juyin mulkin soji da aka yi a Najeriya.

Wadannan jerin juyin mulkin kuwa su ne; Yuli 1966, Fabrairu 1976, Disemba 1983, Disemba 1985 da kuma na watan Afrilu 1990. Har ila yau shi ne wanda ya dauko fadar Shugabancin kasar daga Legas zuwa Abuja a shekarar 1991.

Kamfanin dillacin labarn Najeriya, NAN ta kawo mana wata hira da tayi da marubucin labarin wannan fim, inda ya fadi abinda ya ja ra’ayinsa har ya shirya irin wannan fim haka.

A cikin bayaninsa, Emelonye ya ce, ya zabi labarin IBB ne domin ya farfado da tarihin Najeriya musamman ga yara masu tasowa yanzu. Da kuma sake sanar da su kada daga cikin yadda aka sha fama kafin kafa siyasar Najeriya.

https://www.vanguardngr.com/2019/10/filmmaker-tells-ibbs-story-in-biopic-film-badamosi/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel