Mafi karancin albashi: Gwamnatin Katsina za ta zauna da NLC domin fitar da tsari na musamman

Mafi karancin albashi: Gwamnatin Katsina za ta zauna da NLC domin fitar da tsari na musamman

Gwamnatin jihar Katsina za ta gana kungiyar kwadago (NLC) a kan sabon mafi karancin albashi na naira 30,000. Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Idris Usman Tune ne ya fitar da wannan labari.

Shugaban ma’aikatan, ya fadi wannan maganar ne a wurin wani taro da kungiyar ma’aikatan asibiti da ungozoma ta kasa ta shirya a jihar Katsina, inda ya ce wannan daya daga cikin kudurin gwamnatin na karfafawa ma’aikata kwarin gwiwa a jihar.

KU KARANTA:Uba ya dankarawa diyarsa cikin shege a jihar Gombe

Tune ya ce: “Abin farin ciki ne a ce a yanzu haka babu wata matsala dake tsakanin gwamnati da ‘yan kwadago a jiharmu.”

Shugaban ma’aikatan ya jinjinawa Masari bisa namijin kokarin da yayi wurin kyautatawa ma’aikata daga shekarar 2015 zuwa yanzu. Ya kuma yi kira ga ma’aikata da cewa kada su mayar da hankalinsu kawai a kan aljihunsu, su dage domin ciyar da jiharsu.

A na shi jawabin kuwa, shugaban kungiyar ma’aikatan asibitin reshen jihar Katsina, Haruna Mamman ya yabawa Gwamna Masari a kan wani matsayin da ya bai wa ma’aikatan asibiti wadanda suka karanci aikin nurse.

Mamman ya sake yin kira ga ‘yan kungiyarsa da su dage wurin ganin sun kula kwarai da gaske da marasa lafiya a duk lokacin da aka kawo su asibiti. Ya kuma sake cewa, duk da yake akwai karancin ma’aikatan da kuma kayayyakin aiki, za su yi iya bakin kokarinsu.

https://leadership.ng/2019/10/18/katsina-ready-to-dialogue-with-labour-on-new-minimum-wage/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel