Uba ya dankarawa diyarsa cikin shege a jihar Gombe

Uba ya dankarawa diyarsa cikin shege a jihar Gombe

Wani mutum mai shekaru 72 ya bankawa diyar cikinsa cikin shege a sakamakon fyaden da ya sha yi mata ba sau daya ba, ba sau biyu ba.

Wannan mutum mai suna Ibrahim Danlami Yunusa wanda ke zaune a garin Dadin Kowa dake karamar hukumar Yamaltu Deba a jihar Gombe, ya yiwa diyar da ya haifa cikin shege ta hanyar yi mata fyade da karfin tsiya.

KU KARANTA:Najeriya za ta kuma ciyo bashin dala biliyan 3 daga Bankin duniya, Zainab Ahmad ta fadi dalili

Shekarun yarinyar 17 a duniya, kuma majiyar da ta kawo mana labarin ta ce yarinyar ta bukaci a boye sunanta. A ranar 26 ga watan Satumba, 2019 ne yarinyar ta shigar da karar mahaifinta da yayanta a kotun Bolari, inda ta ce su ne su kayi mata cikin da take dauke da shi.

A cewarta, mahaifinta da yayan nata sun dade suna yi mata fyade a tsakanin watan Disembar 2018 zuwa Janairun 2019, wanda a sakamakon hakan take dauke da cikin wata takwas yanzu.

Kamar yadda yarinyar ta fadi, mahifinta ya soma kwanciyata da ita bayan da ta kai masa karar abinda yayanta ke shigowa dakinta yana yi mata idan dare yayi.

Ta kara da cewa, duk lokacin da taso cijewa a kan kudurin mahaifin nata sai yayi mata barazanar zai koreta daga gidansa. Bayan ta lura da cewa tana dauke da juna biyu ne sai ta yanke shawarar kai karar mahaifinta da yayanta Yusuf Ibrahim zuwa kotu.

“Mahaifina da yayana sun sha kwanciya da ni a lokuta da dama, wannan dalilin ne ya sanya nake dauke da cikin wata takwas. Na sanar da su wannan maganar amma duk sun ki amincewa da maganata.” Inji yarinyar.

Mahaifin yarinyar ya musanta zargin a kotu, inda yake cewa wani direban tasi da ya taba saduwa da yarinyar ne yayi mata cikin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel