Peace Corps: Har yanzu da akwai kyakyawan zaton Buhari zai rattaba hannu - Hadimin shugaban kasa ya bayar da dalilai

Peace Corps: Har yanzu da akwai kyakyawan zaton Buhari zai rattaba hannu - Hadimin shugaban kasa ya bayar da dalilai

Umar Ibrahim El-Yakub, sabon mai taimaka wa shugaban kasa a kan harkokin da suka shafi majalisar wakilai ya yi nuni da cewa har yanzu akwai kyakyawan zaton cewa shugaba Buhari zai iya amince wa da kudirin neman kafa hukumar tsaro ta 'Pace Corps of Nigeria (PCN)'.

Sau biyu shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yana kin saka hannu a kan kudirin nema amincewa da kafa PCN bayan majalisar ta aiko masa a lokutan baya, watau a zangon mulkinsa na farko.

Sai dai, yanzu haka majalisar wakilai ta sake waiwayar kudirin tare da yi masa kwaskwarima domin sake mayar da shi teburin shugaba Buhari domin neman sahalewar sa.

DUBA WANNAN: Mata 2, Maza bakwai: Kotun Kaduna ta saki mabiya Shi'a 9 bayan shekara uku

El-Yakub ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da ya aike wa manema labarai a ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba.

Hadimin na shugaban kasa ya ce: "yanzu an samu kyakyawar alaka tsakanin shugabancin majalisa da fadar shugaban kasa, kuma na tabbata 'yan majalisa zasu aiki a kan kudirin. Tabbas shugaban kasa zai saka hannu a kan kudirin da zarar majalisa ta kammala aiki a kansa, saboda shugaba Buhari bashi da wata boyayyiyar manufa a kan dokokin da majalisa ke kirkira."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel