Aisha Buhari za ta ginawa Kungiyar AFLPM katafaren ofis a Abuja

Aisha Buhari za ta ginawa Kungiyar AFLPM katafaren ofis a Abuja

Uwargidan Shugaban Najeriya, Dr Aisha Muhammadu Buhari a ranar Laraba 16 ga watan Oktoba, 2019 ta fadi cewa za ta gina sakatariya wa Kungiyar matan shugabannin Afirka wadda aka fi sani da African First Ladies Peace Mission (AFLPM).

A shekarar 1995 ne aka kafa wannan kungiyar a karo na farko a birnin Beijing dake kasar China, tun daga lokacin har zuwa yanzu kungiyar na karkashin kulawar Najeriya ne, inda matan shugabannin kasashen Afirka ke musayar jan ragamarta.

KU KARANTA:Tallafin da ake bayarwa bai isowa garemu, manoman shinkafa a Kano sun koka da gwamnatin tarayya

Daraktan yada labaran uwargidan, Suleiman Haruna ne ya fitar da wannan labarin a Fadar Shugaban kasa dake Abuja ranar Laraba, lokaci da matan wadansu gwamnonin Najeriya suka ziyarci Aisha Buhari.

Aisha Buhari ta ce: “Na riga da samu fili mai girman eka 2.7 a nan Abuja inda za a gina sakatariyar matan shugabannin kasashen Afirka. Ba da dadewa ba za a soma gudanar da aikin ginin.”

Da take magana a kan shirin samar da kulawa ta musamman ga mata masu juna biyu da kuma lafiyar abinda suke haifa. Aisha ta ce, akwai alaka mai karfi tsaknin kungiyarsu da kuma gidauniyar uwargidan Bill Gates wanda zuwa karshen shekarar komi zai kankama.

Ta kuma yi amfani da damar ziyarar domin mika godiyarta ga matan gwamnonin bisa irin gudunmuwar da suke kawo na cigaba a jihohinsu, inda ta roke su da su cigaba da yin ayyukan alherin da suka saba.

Har ila yau, ta nemi afuwar ‘yan Najeriya a madadin iyalanta game da bidiyonta dake yawo a shafukan sada zumunta, a kan irin abinda wannan faifan bidiyo ya jawowa kasar a fadin duniya.

https://www.vanguardngr.com/2019/10/aisha-buhari-to-build-secretariat-for-african-first-ladies/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel