APC jam'iyya ce ta gagaruman makaryata - Gwamnan PDP

APC jam'iyya ce ta gagaruman makaryata - Gwamnan PDP

Gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade ya bayyana jam’iyyar All Progressives Congress wato APC a matsayin jam’iyya wadda ke cike da makaryata musamman ma a jiharsa.

Gwamnan ya ce maganganun da shugaban APC, John Ochala yayi game da komawarsa jami’a abin dariya ne. A cewar Ayade yadda APC ta zama abin dariya a Cross River haka wannan maganar ta shugabansu ta zama.

KU KARANTA:Karancin wurin zama: Gwamnatin tarayya za ta gina gidaje 30,000 a sassan Najeriya daban-daban

Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun kawo mana labarin cewa, Ochala ya bayyana komawar Gwamna Ayade makaranta a matsayin gazawa da kuma rashin sanin yadda ake jagoranci, inda a cewarsa abinda ya je koya kenan a jami’ar.

Sai kuwa Gwamnan ya bayar da nashi martanin game da wannan maganar a wani zancen da hadiminsa a kan lamuran labarai, Christian Ita ya fitar, ya ce: “Abin dariya ne a ce jam’iyya kamar APC dake daukar kanta a matsayin babba ta gaza yin muhawara a siyasance sai dai karya domin ta samu yabo.

“Idan har APC bata ga laifin Gwamna Nasir El-Rufai a lokacin da ya tafi kasar Netherlands domin yin digirin PhD, me yasa yanzu za a ga laifin Gwamna Ayade don ya koma jami’a domin karo ilimi, kuma Calabar ba ma kasar waje ba?” Inji shi.

Haka zalika zancen ya tunawa APC, Sanata Orji Uzor Kalu na APC a lokacin da yake gwamnan Abia bai kammala digirinsa na farko ba jami’a. Yana gwamnan yana karatunsa a wancan lokacin.

Zancen ya cigaba da cewa, komawar Gwamna Ayade makaranta abin a yaba ne, kasancewar bai fita wata kasar ba a gida Najeriya ya tsaya kuma a jami’ar dake jiharsa. Ba kamar yadda gwamnonin APC ke tsallakawa turai ba.

https://www.dailytrust.com.ng/apc-party-for-notorious-liars-gov-ayade.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Must end with a letter, digits, period, question or exclamation mark, closing quote or bracket.

Asali: Legit.ng

Online view pixel