Gwamnan Bauchi ya yi karin haske akan furucinsa na cewa daga Allah sai Jonathan

Gwamnan Bauchi ya yi karin haske akan furucinsa na cewa daga Allah sai Jonathan

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya yi karin haske akan furucin da ya yi kwanan nan wanda ya kawo cece-kuce a ciki da wajen jihar cewa "bayan Allah, sai tshon shugaban kasa Goodluck Jonathan."

Gwamnan ya yi furucin ne a lokacin kaddamar da kungiyar kamfen din jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na zaben gwamnan jihohin Bayelsa da Kogi a sakatariyar jam'iyyar na kasa dake Abuja.

An alakanta shi da fadin cewa, a iya saninsa bayan Allah toh Goodluck Jonathan ne, lamarin da ya kawo cece-kucea shafukan sadarwa.

Da yake jawabi ga manema labarai akan lamarin, kwamishinan labarai na jihar, Ladan Salihu, wanda yayi karin hasken akan matsayar ubangidan nasa, ya bayyana cewa a koda yaushe Gwamna Bala Muhammed kan sa Allah da annabi Muhammed a gaba kafin yayi kowani furuci.

Ya yi bayanin cewa jawabin da gwamnan yayi ba wani sabon abu bane kawai jawabi ne na siyasa sannan ya bata rai kan yadda aka canja fassarar abun har ta kai ana alakanta lamarin ga addini.

Ya bayyana cewa an yiwa furucin mummunan fahimta ne sannan kuma cewa baya dauke da ainahin sakon, inda ya kara da cewa kawai gwamnan na yabon tsohon shugaban kasar ne wanda ya bayyana a matsayin gwaninsa a harkar siyasa da ya bashi damar yiwa kasasa hidima a matsin ministan Abuja a lokacin gwamnatinsa.

KU KARANTA KUMA: Kasafin 2020: Sanata Ndume ya yi korafi akan kudin da aka warewa sojoji

Kwamishianan ya roki masu tayar da fitina da su janye daga amfani da jawabin wajen cimma burinsu na siyasa domin a koda yaushe gwamnan zai kasance mai mutunta addininsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel